Posts

Showing posts from February 17, 2024

Shugabannin duniya na alhinin rasuwar Navalny

Image
Reuters Copyright: Reuters Shugabannin ƙasashen duniya na ci gaba da alhinin rasuwar jagoran adawar Rasha Alexei Navalvy. Mista Navalny ya rasu ne a ɗaya daga cikin gidajen yari mafiya tsaro a ƙasar, inda yake zaman hukuncin da aka yanke masa. Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya ce ga alamu jagoran adawar Rashan ya rasa ransa ne saboda jarumtakarsa. Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak, ya ce Mista Navalny ya kasance na gaba wajen hanƙoron kawo da Dimokradiyya a Rasha. Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, shugabannin ƙasashen kungiyar tarayyar Turai sun ce sannu a hankali gwamnatin Putin ta kashe Mr Navalny. Hukumar kare hakkin ɗan'dam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta kaɗu da samun labarin mutuwarsa, ta na mai cewa idan har mutum ya mutu a lokacin da ake tsare da shi to ana danganta mutuwar tasa da laifin gwamnatin ƙasar da yake tsaren.

Issoufou na da hannu a cire Bazoum daga mulki – Tsohon jakadan Faransa

Image
ASALIN HOTON, OTHER Sa'o'i 3 da suka wuce Kikitsa juyin mulkin ko kuma ya goyi bayan hambarar da shugaba Bazoum, zargin da wani makusancin tsohon shugaban ƙasar ya musanta. Tsohon jakadan na Faransa a Jamhuriyar Nijar, Sylvain Itté ya yi wata ganawa ne ta sirri da ‘yan kwamitin da ke kula da harkokin tsaron kasar da kuma dakarunta a majalisar dokokin Faransa a Paris domin ba su bahasi kan abin da ya kai ga juyin mulkin da sojoji suka yi a a Nijar a shekarar da ta gabata. A bayannin da tsohon jakadan ya yi wa ‘yan majalisar ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban Nijar Mohammadou Issoufou, ya goyi bayan hambarar da mutumin da ya gaje shi Mohammed Bazoum saboda wani sabani da suka samu a tsakaninsu da ke da alaƙa da kuɗin mai na ƙasar

An jahilci manufar samar da ƴansandan jihohi a Najeriya - Uba Sani

Image
Sa'o'i 3 da suka wuce Gwamnan jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya Sanata Uba Sani ya ce wasu sun jahilci manufar samar da ƴansandar jiha da ake cecekuce akai a ƙasar. A makon nan ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da a duba yiwuwar kafa rundunar ƴansandan jihohi a ƙasar a matsayin wani mataki na shawo kan matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa. Shugaban ya amince da haka ne bayan ganawa da ya yi da gwamnonin jihohin ƙasar 36, inda Tinubu ya buƙaci gwamnonin su fara tsara yadda za a aiwatar da shirin. Gwamnan Kaduna daya daga cikin masu fama da kalubalen yanbindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa ya ce akwai ƙarancin ƴansanda a Najeriya, kuma samar da ƴansandan jihohi zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya. TALLA "Yawan ƴansandan da ake da su a ƙasar nan bai kai yadda za su iya kare al'umma ba, kuma babu wani gwamna a jiharsa da yake iya ba kwamishinan ƴansanda umarni," in ji Gwamna Uba Sani