An jahilci manufar samar da ƴansandan jihohi a Najeriya - Uba Sani
Gwamnan jihar Kaduna a arewa maso yammacin Najeriya Sanata Uba Sani ya ce wasu sun jahilci manufar samar da ƴansandar jiha da ake cecekuce akai a ƙasar.
A makon nan ne Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya amince da a duba yiwuwar kafa rundunar ƴansandan jihohi a ƙasar a matsayin wani mataki na shawo kan matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa.
Shugaban ya amince da haka ne bayan ganawa da ya yi da gwamnonin jihohin ƙasar 36, inda Tinubu ya buƙaci gwamnonin su fara tsara yadda za a aiwatar da shirin.
Gwamnan Kaduna daya daga cikin masu fama da kalubalen yanbindiga masu satar mutane domin kuɗin fansa ya ce akwai ƙarancin ƴansanda a Najeriya, kuma samar da ƴansandan jihohi zai taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.
"Yawan ƴansandan da ake da su a ƙasar nan bai kai yadda za su iya kare al'umma ba, kuma babu wani gwamna a jiharsa da yake iya ba kwamishinan ƴansanda umarni," in ji Gwamna Uba Sani
Comments