Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano
Copyright: Other Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan al’amarin da ya biyo bayan zargin fille kan wani karamin yaro ɗan shekara shida da wani almajiri ya yi a kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Madobi. Rahotanni dai sun nuna cewa almajirin mai shekaru 22 ya kashe yaron ne a kusa da wata makarantar firamare kafin ya cire kansa. Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya shaida wa BBC cewa almajirin bayan ya yanke wa yaron kai ya jefa da kan a cikin wani masai. "A jiya ne aka wayi gari da wannan labari da ke cewa wasu masu ruwa da tsaki suka lura da cewa sun ga wani yaro a wannan ƙauye da wuƙa wanda suka ga alamun jini a jikin wuƙar kamar jinin ɗan Adam ne, Hakan ne ya sa suka zarge abin da ya sa 'yan unguwa suka cafke shi, suka tasa shi gaba, sai suka ga gangar jikin mutum inda ya amsa shi ne ya kashe shi. Bayan da ƴan sanda suka je, shi ne ya ja su ya kai su inda ya wurgar da kan, inda suka ga kan yaron." In ji kwamishinan 'ya...