Matsalar hare-haren ƴan bindiga ta ɗauki sabon salo a jihar Zamfara
ASALIN HOTON, OTHERS Sa'o'i 3 da suka wuce A Najeriya, hare-haren da ƴan bindiga ke kaiwa garuruwa da ƙauyuka a jihar Zamfara ya ɗauki sabon salo, sakamakon yadda suka fara mayar da hankali ga yi wa matan aure fyaɗe a gidajen mazajensu da aikata kisan gilla, da dai sauran ayyukan ta'asa a garin Kalgon Ƙunci na yankin karamar hukumar Tsafe. Lamarin ya sa kashi kimanin saba'in cikin ɗari na jama’ar garin sun tsare zuwa wasu wurare. Yayin da jama'a suka sabunta kyakkyawan fatan samun saukin matsalar tsaro, bayan ƙaddamar da rundunar kare fararen hula a jihar Zamfara, ƴan bindiga sun sauya wa gyambo kafa, a garin Kuncin Kalgo na yammacin yankin karamar hukumar Tsafe. Kamar yadda wani mutumin garin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC: ‘‘A da dai za su shigo cikin garin mu, su wulaƙanta mu, su saci dabbobi, su yi garkuwa da mutane. To yanzu da ranar Allah za su shigo garin mu, kuma ba su fita sai ƙarfe sha biyu da dare, da makaman su tunda mutum ɗaya za ka ga ...