Ɗantakarar shugaban Senegal na jam'iyya mai mulki ya taya na adawa murna
Bassirou Diomaye Faye Yayin da al'ummar ƙasar Senegal ke jiran hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar Lahadi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki Amadou Ba ya taya ɗan takara na haɗakar ƴan adawa Bassirou Diomaye Faye murnar samun nasara. Alƙaluman da jam'iyyun siyasar ƙasar ke tattarawa bayan rufe rumfunan zaɓe a jiya Lahadi sun nuna cewa Bassirou Faye na jam'iyyar adawa shi ne ke kan gaba a yawan ƙuri'un da za su iya ba shi nasara kai-tsaye. Har yanzu dai babu wani sakamako da ya fito daga hukumar zaɓen ƙasar, wadda ke ci gaba da tattara sakamakon, kuma ba za ta bayyana ƙuri'un da kowane ɗantakara ya samu ba sai ta kammala haɗa alƙaluma. Taya Faye murna da Amadou ya yi ya zo wa al'umma da mamaki, ganin irin hamayya mai ƙarfi da ke tsakanin ɓangarorin biyu. A cikin sanarwar da ya fitar, Amadou Ba ya ce: "Ganin irin bayanan da ke fitowa game da zaɓen shugaban ƙasa, yayin da muke ci gaba da jiran ...