Ɗantakarar shugaban Senegal na jam'iyya mai mulki ya taya na adawa murna


 

Bassirou Diomaye Faye

Yayin da al'ummar ƙasar Senegal ke jiran hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar Lahadi, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyya mai mulki Amadou Ba ya taya ɗan takara na haɗakar ƴan adawa Bassirou Diomaye Faye murnar samun nasara.


Alƙaluman da jam'iyyun siyasar ƙasar ke tattarawa bayan rufe rumfunan zaɓe a jiya Lahadi sun nuna cewa Bassirou Faye na jam'iyyar adawa shi ne ke kan gaba a yawan ƙuri'un da za su iya ba shi nasara kai-tsaye.


Har yanzu dai babu wani sakamako da ya fito daga hukumar zaɓen ƙasar, wadda ke ci gaba da tattara sakamakon, kuma ba za ta bayyana ƙuri'un da kowane ɗantakara ya samu ba sai ta kammala haɗa alƙaluma.


Taya Faye murna da Amadou ya yi ya zo wa al'umma da mamaki, ganin irin hamayya mai ƙarfi da ke tsakanin ɓangarorin biyu.


A cikin sanarwar da ya fitar, Amadou Ba ya ce: "Ganin irin bayanan da ke fitowa game da zaɓen shugaban ƙasa, yayin da muke ci gaba da jiran sakamako a hukumance, ina taya shugaba Bassirou Diomaye Faye murna kan nasarar da ya samu tun a zagayen farko,


"Ina roƙon Allah ya ba shi ƙarfin ikon tafiyar da harkokin wannan ƙasa tamu. Ina roƙar masa nasara da kuma nasarar dukkanin al'ummar Senegal."


Bassirou Diomaye dai shi ne ɗantakarar da madugun adawa Ousmane Sonko ya mara wa baya, bayan haramta masa tsayawa takara.


Dama dai tuni ƴan takarar shugaban ƙasar 17 suka taya Bassirou Faye murna, bayan da sakamako ya fara fitowa daga sassan ƙasar.


A lokacin yaƙin neman zaɓe Faye ya bayyana kansa a matsayin wanda zai kawo sauyi a ƙasar ta yammacin Afirka mai yawan mutane miliyan 18.


Cikin alƙawurran da ya yi har da rage biyayyar da Senegal ɗin ke yi wa uwargijiyarta Faransa da kuma daina amfani da takardar kuɗi ta CFA.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano