ba fada ba komai mijina bayan yayi sallar Asuba ya mikomin takardar saki, kuma Wallahi lafiya lau muke, jiya tare muka ci Abincin dare muna cu muna hira ina ta saka shi nishada da walwala, don kwanan nan sai Naga ya zauna shi kadai Yana tunani kamar Yana da damuwa in na tambaye shi sai yace ba komai. Da na karanta takardar na dago kai muka hada ido idanuwa na cike da kwalla nace masa wane mai nayi Maka ? Mai yayi zafi haka? Sai yace min zama ne ya kare kawai . Nayi hakuri. Da ya ga kukana ya tsanan ta sai yace wance kiyi hakuri ba son kine bana yiba, Amman Malamai na sun tabbatar min da cewa in har ina tare dake bazantaɓa yin arziki ba, sai dai na samu mai suna Safiyyya na aura shine burujin sunan mu zai haɗu. Malama Ya zanyi? Ni marainiyata ce , yarana uku,yanzu ma watana biyu da haihuwa ta ukun. Babata da babana duk sun rasu na rasa yadda zanyi.😭 Kanawapostnews