Copyright: NDLEA/X Jami'an Hukumar da ke Hana sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Najeriya (NDLEA) ta cafke wani fasinja a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke jihar Legas ɗauke da kullin hodar iblis guda 80. An kama Ogbonna ne a ranar Lahadi, 31 ga Maris, 2024, a lokacin da yake yunkurin hawa jirgin Qatar Airways zuwa birnin Delhi na ƙasar Indiya, ɗauke da fasfo ɗin ƙasar Laberiya. NDLEA ta bayyana kama mutumin ne a wata sanarwa da kakakinta Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi. Babafemi ya ce an yi wa wanda ake zargin gwaje-gwaje, inda aka gano cewa yana tu'amalli da miyagun kwayoyi. “Mun yi mamaki da muka gano yawan kwayoyi da a haɗiye a cikinsa, nan da nan ya fara yin amai na kullin hodar iblis da ya haɗiye," in ji Babafemi. NDLEA ta ce mutumin da ake zargi ya yi iƙirarin cewa wani dan uwansa ne ya ɗauke shi aiki don ya rika safarar kwayoyi. An kuma samu ɗaurin hodar iblis guda 80 mai nauyin kilogram 889 a wajensa wanda ya amayar cikin kwanaki huɗu. “Abin da ya ...
HOTONAN Yadda Kabilar Dakarkari ke cigaba da gudanar da wasannin al'adun Gargajiya Zuru Uhola. Bikin raya al'adun Gargajiya na kabilar Dakarkari dake masarautar Zuru a jihar kebbi biki ne da ake gudanarwa domin nuna godiya ga Allah. Dubban al'umma ne ciki da wajen jihar suka halarci taron ciki hadda dan majalisar tarayyar Najeriya mai wakiltar masarautar Zuru Hon Kabir Ibrahim Tukura. Hoto📷 Abbakar Aleeyu Anache
Babban hafsan sojin Najeriya Janar Christopher Musa Image caption: Babban hafsan sojin Najeriya Janar Christopher Musa Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gargaɗi masu kiraye-kirayen juyin mulki sakamakon matsin rayuwa, inda ya ce haƙuri abu ne mai muhimmanci a mulkin dimokuraɗiyya. Janar Musa ya bayyana hakan ne yau Alhamis, yayin da yake ganawa da ƴan jarida a birnin Fatakwal na jihar Ribas, bayan ƙaddamar da ayyukan wasu gine-gine. Babban hafsan sojin ya buƙaci masu furta irin waɗannan kalamai da su daina. An dai gudanar da jerin zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa a jihohin Kano da Oyo da Ogun a ƙasar ta Najeriya, yayin da mutane ke ci gaba da kokawa kan tsadar kayan masarufi. Najeriya na fama da hauhawar farashin kayan masarufi da sufuri da kuma ƙarancin kuɗaɗen shiga. Bugu da ƙari darajar takardar kuɗin naira na ci gaba da zubewa idan aka kwatanta da dalar Amurka, wadda ke da matuƙar tasiri a ɓangaren tattalin arziƙi na ƙasar. Ana dai ɗora ...
Comments