Zan yi murabus idan na gaza kai ƙarshen binciken Yahaya Bello – Shugaban EFCC
Zan yi murabus idan na gaza kai ƙarshen binciken Yahaya Bello – Shugaban EFCC Copyright: EFCC/X Shugaban hukumar EFCC da ke yaƙi da masu yi wa arzikin Najeriya zagon ƙasa, Ola Olukoyede ya sha alwashin yin murabus idan na gaza gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello. A wani taron tattaunawa da zaɓaɓɓun editoci a hedikwatar hukumar da ke Abuja, babban birnin Najeriya, shugaban hukumar ya yi alƙawarin hukunta duk masu kawo kawo tarnaƙi ga kama tsohon gwamnan. A ranar 18 ga watan Afrilu, EFCC ta ayyana Bello a matsayin wanda take nema ruwa a jallo saboda zarginsa da badaƙalar kuɗi ta naira miliyan 80. Yahaya Bello dai bai bayyana gaban kotu ba tun bayan ayyana ana nemansa ruwa a jallo. Shugaban EFCC ya ce da kansa ya kira Bello cikin mutunci inda ya nemi da ya bayyana gaban hukumar ya kuma yi bayani kan tuhume-tuhumen da ake masa. Shugaban EFCC ya ce duk da kiran wayar, tsohon gwamnan bai amsa gayyatar ba. Yahaya Bello dai ya musanta gayyatar da aka yi masa inda ya ƙalu...