Yadda gwamnatin jihar Katsina ta rarraba wa jami'an tsaro motocin yaƙi
ASALIN HOTON, KATSINA STATE GOVERMENT Bayani kan maƙala Marubuc Sanya sunan wanda ya Gwamnatin jihar Katsina ta rarraba motocin yaƙi ga jami'an tsaro domin shawo kan matsalar tsaro a ƙananan hukumomin da aka fi fuskantar hare-haren ƴanbindiga. Gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda ne ya ƙaddamar da rabon motocin a ranar Litinin. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Katsina, Dakta Nasiru Mu'azu ya shaida wa BBC cewa sun yi la'akari ne da halin da ake ciki, kuma ita wannan mota mai sulke na taimaka wa wajen yaƙin da suke da ƴan bindiga. Gwamnatin ta jihar Katsina ta rarraba motocin guda 10 ne ga jami'an tsaro na ƴan sanda da sojoji da kuma ƴan sa-kai da gwamnatin ta dauka a kwanakin baya domin taimakawa wajen yaƙi da ƴan bindiga a jihar." ASALIN HOTON, KATSINA STATE GOVERMENT Mun yi maganin masu bai wa ƴan bindiga bayanai-Gwamna Dikko Radda 11 Fabrairu 2024 Gane Mini Hanya tare da Gwamnan Katsina Dikko Radda 21 Oktoba 2023 'Ƴanbindiga ...