Yadda gwamnatin jihar Katsina ta rarraba wa jami'an tsaro motocin yaƙi

 

Motocin yaƙi da gwamnatin jihar Katsina ta raba

ASALIN HOTON,KATSINA STATE GOVERMENT

  • Marubuc
  • Sanya sunan wanda ya

Gwamnatin jihar Katsina ta rarraba motocin yaƙi ga jami'an tsaro domin shawo kan matsalar tsaro a ƙananan hukumomin da aka fi fuskantar hare-haren ƴanbindiga.

Gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda ne ya ƙaddamar da rabon motocin a ranar Litinin.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Katsina, Dakta Nasiru Mu'azu ya shaida wa BBC cewa sun yi la'akari ne da halin da ake ciki, kuma ita wannan mota mai sulke na taimaka wa wajen yaƙin da suke da ƴan bindiga.

Gwamnatin ta jihar Katsina ta rarraba motocin guda 10 ne ga jami'an tsaro na ƴan sanda da sojoji da kuma ƴan sa-kai da gwamnatin ta dauka a kwanakin baya domin taimakawa wajen yaƙi da ƴan bindiga a jihar."

Motocin yaƙi da gwamnatin jihar Katsina ta raba

ASALIN HOTON,KATSINA STATE GOVERMENT

Gwamnan jihar Katsina da jami'ansa

ASALIN HOTON,KATSINA STATE GOVERMENT

Dakta Mu'azu ya ce ƙananan hukumomin da aka ba motocin sun hada da Jibiya da Safana da Ɗanmusa da Ƙanƙara da Batsari da Faskari da Ɗandume da kuma Sabuwa, "lokacin da muka zo bisa mulki ƙananan hukumomi 23 ne ke fuskantar matsalar tsaro, amman yanzu wadannan ƙananan hukumomin ne kawai suka rage sai kuma Kurfi da ita ma muke ƙoƙarin dakile lamarin da ya soma faruwa."

Kwamishinan ya ce daman ƙananan hukumomin na da irin wadannan motoci, kawai ƙari ne aka yi masu saboda a ƙara samun cigaba wajen ƴakin da ake da ƴanbindiga.

Jihar Katsina dai na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fama da matsalar tsaro musamman ta ‘yan fashin daji wadanda ke kai hare-hare garuruwa da kauyukan jihar baya ga satar mutane don neman kudin fansa da kuma sace dukiyoyin mazauna yankin.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano