Posts

Showing posts from February 22, 2024

Babban hafsan sojin Najeriya ya gargaɗi masu neman a yi juyin mulki

Image
Babban hafsan sojin Najeriya Janar Christopher Musa Image caption: Babban hafsan sojin Najeriya Janar Christopher Musa Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gargaɗi masu kiraye-kirayen juyin mulki sakamakon matsin rayuwa, inda ya ce haƙuri abu ne mai muhimmanci a mulkin dimokuraɗiyya. Janar Musa ya bayyana hakan ne yau Alhamis, yayin da yake ganawa da ƴan jarida a birnin Fatakwal na jihar Ribas, bayan ƙaddamar da ayyukan wasu gine-gine. Babban hafsan sojin ya buƙaci masu furta irin waɗannan kalamai da su daina. An dai gudanar da jerin zanga-zangar nuna damuwa kan tsadar rayuwa a jihohin Kano da Oyo da Ogun a ƙasar ta Najeriya, yayin da mutane ke ci gaba da kokawa kan tsadar kayan masarufi. Najeriya na fama da hauhawar farashin kayan masarufi da sufuri da kuma ƙarancin kuɗaɗen shiga. Bugu da ƙari darajar takardar kuɗin naira na ci gaba da zubewa idan aka kwatanta da dalar Amurka, wadda ke da matuƙar tasiri a ɓangaren tattalin arziƙi na ƙasar. Ana dai ɗora ...

Shin samamen jami’an tsaro a kasuwannin canji zai farfaɗo da darajar naira?

Image
A cikin 'yan kwanakin nan ne hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati a Najeriya ta soma kai samame kan masu hada-hadar canjin kuɗi a sassan ƙasar a wani mataki na kawo maslaha ga yadda farashin dala ke hauhawa yayin da darajar naira kuma take ƙara raguwa. EFCC ta kai irin wannan samame kan masu sana'ar canji a biranen Abuja da Legas da Kano da Ibadan da kuma Fatakwal inda ta kama da wadansu masu sana'ar ta canji. Ko a ranar Larabar da ta wuce, sai da farashin dala ya kai naira 1,850 a kasuwar ta bayan fage a Abuja, lamarin da ke ƙara jefa mutane cikin zullumi ganin yadda abun ke ƙara janyo tsadar kayayyaki a kasuwa. Ya zuwa ranar Alhamis, a hukumance ana sayar da dalar Amurka ne kan naira 1,650. Baya ga ƴan canji, wasu da ake zargi da hannu kan zuzuta farashin dalar a kullum su ne kamfanonin hada-hadar kuɗin intanet na kirifto. Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana ɗaukar duka matakan da suka dace domin daidaita darajar naira tare da magan...

Yadda kamfanonin kirifto ke haddasa tashin farashin dala a Najeriya

Image
Yadda kamfanonin kirifto ke haddasa tashin farashin dala a Najeriya ASALIN HOTON, GETTY IMAGES Sa'o'i 4 da suka wuce Gwamnatin Najeriya na duba yiwuwar hana kamfanin kirifto na Binance da sauran kamfanonin hada-hadar kuɗaɗen intanet yin hada-hada da kuɗin ƙasar, domin dakatar da abin da ta kira 'yawaitar' tashin farashin kuɗin ƙasar waje. Wannan na zuwa ne sakamakon tashin gwauron zabi da farashin kuɗin ƙasar waje ke yi a Najeriya, inda wasu ke zargin kamfanin Binance da sauran kamfanonin kuɗin intanet da yin uwa da makarɓiya wajen saka farashin dalar. Da dama daga cikin 'yan ƙasar na zargin cewa masu hada-hadar kuɗin kan duba shafin Binance da ake sabunta bayanai a kowace rana domin sanin farashin da za sayar da kudin kasar wajen. Yawaitar faraduwar darajar kuɗin Najeriya a baya-bayan nan na ci gaba da haddasa fargaba a zukatan 'yan ƙasar, inda farashin kayayyaki ke cigaba tashin gawauron zabo, lamarin da ya jefa ...