Shin samamen jami’an tsaro a kasuwannin canji zai farfaɗo da darajar naira?

A cikin 'yan kwanakin nan ne hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati a Najeriya ta soma kai samame kan masu hada-hadar canjin kuɗi a sassan ƙasar a wani mataki na kawo maslaha ga yadda farashin dala ke hauhawa yayin da darajar naira kuma take ƙara raguwa.

EFCC ta kai irin wannan samame kan masu sana'ar canji a biranen Abuja da Legas da Kano da Ibadan da kuma Fatakwal inda ta kama da wadansu masu sana'ar ta canji.

Ko a ranar Larabar da ta wuce, sai da farashin dala ya kai naira 1,850 a kasuwar ta bayan fage a Abuja, lamarin da ke ƙara jefa mutane cikin zullumi ganin yadda abun ke ƙara janyo tsadar kayayyaki a kasuwa.

Ya zuwa ranar Alhamis, a hukumance ana sayar da dalar Amurka ne kan naira 1,650.

Baya ga ƴan canji, wasu da ake zargi da hannu kan zuzuta farashin dalar a kullum su ne kamfanonin hada-hadar kuɗin intanet na kirifto.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce tana ɗaukar duka matakan da suka dace domin daidaita darajar naira tare da magance yawan tashin da farashin dala ke yi, ciki har da yunƙurin rufe kamfanonin na kirifto.

Wane tasiri waɗannan matakan ke da shi ga halin da naira ta shiga da kuma tashin farashin dala?

'Ba mu EFCC ke kai wa samame ba'

Shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar canji a Najeriya, Aminu Gwadabe ya ce samamen da EFCC ke kaiwa kan masu hada-hadar musayar kuɗi mataki ne da ya shafi masu sana'ar ba tare da lasisi ba musamman waɗanda ke saye da sayar da dala a bakin titi.

Shugaban ƙungiyar ya shaida wa BBC cewa tun farko gwamnati tana yawan tattaunawa da shugabannin ƴan canji - masu lasisi da waɗanda ba su da shi inda ta sha gargaɗi a kan yadda wasu ke sayar da dala ba tare da samun amincewar gwamnati ba.

A cewarsa da alama gwamnati ta kai maƙura a yadda matsalar ta ƙi ci ta ƙi cinyewa abin da ya sa ta ɗauki matakin domin ko dai a kawo gyara "ko kuma a daina ta."

Aminu Gwadabe ya ce a tattaunawar da suke yi da gwamnati, sun samu bayanin cewa "kuɗaɗen gwamnati da yawa da ake kwashewa ko ake satar su ana [alaƙanta] su ga ƴan canjin da yawancinsu ba su da lasisi."

"Kuma idan ka san ƙasar a yanzu, abin da ake faman yaƙi da shi ke nan - cin hanci da rashawa da ta'addanci da sace-sacen mutane," in ji shi.

Ya ce bayanan da hukumomi suka yi shi ne "waɗanda ke aikata miyagun laifuka na amfani da damar wajen tsoratar da mutane tare da ɓatar da kuɗaɗen cin hanci da rashawa da ta'addanci."

...

Akwai sauran rina a kaba...

Wani masanin hada-hadar kuɗin kirifto a Najeriya, Muhammad Inuwa Aliyu ya ce matakin da EFCC da jami'an tsaron Najeriya ke ɗauka na kai samame a kasuwannin canji kuɗi "alama ce ta cewa ba a shirya kawo ƙarshen matsalar ba saboda kamar mutum ne mai fama da ciwon kai sai a ba shi maganin ciwon ciki."

A cewarsa, matsala ce da tun farko gwamnati ta soma janyo ta bayan da ta bijiro da tsarin da barin kasuwa ta tantance darajar naira, abin da ke nufin "kowa zai iya sayar da dala yadda ya ga dama."

Sai dai ya ce duk da haka harkar ƴan kirifto ta taka rawa sosai ga halin da darajar naira ke ciki da kuma hauhawar farashin dala.

Amma ya ce a ɓangare ɗaya kuma an fara ganin tasirin matakan da gwamnati ta ɗauka daga ranar Laraba, inda farashin dala ya fara sauka - "ta ɗan rage naira 250".

A cewarsa, idan gwamnati ta ci gaba da ɗaukan irin waɗannan matakai, darajar kuɗin Najeriya za ta ƙaru sannan za a kawo sauƙi ga yadda farashin dalar ke tashi.

Masanin ya ce ya zama dole gwamnati ta janye matakin da ta ɗauka na barin naira ta nemi darajarta a kasuwa abin da ya ce shi ne silar durƙushewar tattalin arzikin Najeriya.

Yadda za a farfaɗo da darajar naira a Najeriya

Masani Muhammad Inuwa Aliyu ya ce batun farfaɗo da ƙimar naira "ya ƙunshi abubuwa da dama" saboda Babban bankin Najeriya CBN yana da rawar da zai taka a kan haka.

Ya bayyana cewa "idan CBN ya ƙara darajar naira, idan suka zo suka mayar da ita, misali suka ce dala ɗaya suna so ta tsaya a 800, to su kansu kamfanonin musayar kuɗi na intanet, sai ka ga abin ya sauko."

Ya bayar da misali da yadda a cikin watan Janairu aka karya darajar naira ya zama dala ɗaya ta kai naira fiye da dubu ɗaya, "daga nan ne ake samun giɓi a kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet tun da ba farashinsu ɗaya da gwamnati ba."

A cewarsa, ya kamata gwamnati ta cike giɓin da ake samu tsakanin farashin hukuma da na ƴan canji saboda "in dai ba a kulle wannan giɓi ba, gaskiya ba abin da gwamnati za ta iya yi a kan dala,"


"Saboda ba ta da iko kan kuɗaɗen da mutane suke da shi a gida suka ajiye, ba ta da iko kan kamfanonin hada-hadar kuɗi ta intanet saboda abu ne mai wahala ka iya hana abu a intanet." in ji masanin.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano