gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake nada amb Yusuf imam ogan ɓoye

gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake nada amb Yusuf imam ogan ɓoye

 a matsayin Mai bashi shawara akan harkokin matasan da wasanni  tare da wasu mutum takwas Wanda zasu taimakawa Gwamnan a fanno daban daban .


A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, a Wanan Rana yace Gwamnan ya amince da nada


 1. Farfesa Ibrahim Magaji Barde, a matsayin mai bashi shawara na musamman kan harkokin tattara kudaden shiga (IGR).


 2. Dr. Abdulhamid Danladi, mai bashi shawara na musamman kan harkokin kasashen waje II


 3. Engr.  Bello Muhammad Kiru, mai bashi shawara na musamman kan albarkatun ruwa.


 4. Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) ya sake nada shi a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni.


 5. Dr. Nura Jafar Shanono an dauke shi daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Darakta, a ma.aikatar Ruwa da Gine-gine (WRECA).


 6.Haka kuma Baba Abubakar Umar ya samu sauyi daga mai bawa gwamna Kano shawara na musamman ga harkokin makarantu masu zaman kansu zuwa aikatar dake kula da ma.aikatan hucin gadi


 7. Hon.  Nasir Mansur Muhammad an nada shi shugaban hukumar , Kanana da Matsakaitan Masana'antu (SMEs).


 8. Aminu Hamidu Bako Kofar Na’isa zai zama mataimakin shugaban Hukumar kula da Albarkatun Noma  Raya Karkara ta Kano (KNARDA).


 9. Engr.  Mukhtar Yusuf, Mataimakin shugaban hukumar kula Albakatun ruwa Ruwa da Gine Gine (WRECA).


Sanarwar tace Nadin ya fara aiki nan take, Kuma Gwamnan ya taya su murna tare da fatan alkhairi

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano