Posts

Showing posts from February 9, 2024

Abubuwan da JNI ta faɗa kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Image
Sa'a 1 da ta wuce Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta nuna damuwa kan matsalar hauhawan farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a Najeriya. Kungiyar ta bukaci mahukuntam kasar da su  gaggauta daukar matakan tallafawa al’umma don rage musu wahalhalu da suke fama da su. A cikin wata sanarwa da ta fitar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin mai alfarma sarkin musulmi Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku ta ce abin damuwa ne kan yadda wasu al'umma suka fara zanga-zanga sakamakon mawuyacin halin da suke ciki. Ta ce yadda mutane suka fara harzuƙa na nuna cewa tura ta kai bango, kuma ishara ce ga mahukunta su ɗauki matakin gaggawa domin gudun kada al'ammura su gagari kundi Ta bukaci gwamnati da ta gaggauta daukar matakan tallafawa al’umma don rage musu raɗaɗi.