Abubuwan da JNI ta faɗa kan tsadar rayuwa a Najeriya.


Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta nuna damuwa kan matsalar hauhawan farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a Najeriya.

Kungiyar ta bukaci mahukuntam kasar da su  gaggauta daukar matakan tallafawa al’umma don rage musu wahalhalu da suke fama da su.

A cikin wata sanarwa da ta fitar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin mai alfarma sarkin musulmi Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku ta ce abin damuwa ne kan yadda wasu al'umma suka fara zanga-zanga sakamakon mawuyacin halin da suke ciki.

Ta ce yadda mutane suka fara harzuƙa na nuna cewa tura ta kai bango, kuma ishara ce ga mahukunta su ɗauki matakin gaggawa domin gudun kada al'ammura su gagari kundi

Ta bukaci gwamnati da ta gaggauta daukar matakan tallafawa al’umma don rage musu raɗaɗi.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano