Posts

Showing posts from April 5, 2024

Lalle anci zarafin iyayanmu.. Yazama dole mununa damuwarmu akai

Image
    Wannan wata gurbatacciyar Dabi. Ace Wanda masu kudin mu da yan siyasarmu keyi.. Wanda basa banbance iklasi dakuma riya    Wanda mafi yawansu zuciyoyinsu Sun cika da tunanin yin aiki koh gudanar da wani abuh domin afadi alkairinsu  batareda Sun San riya Tashiga aikinsuba  Idan muka kalla zamuga wayan nan kakan nin wasu NE iyaye GA wasu  Yazakaji idan dan siyasa yabawa wani naka abinci yadaukeshi a hoto yadora a  media duniya tagani  Yan media gareku bakuda wani amfani sede in Mai gidanka yasaka kazagi wancan Kaci mutuncin wancan ka yabi wancan shine aikinka bakada tunanin kallon matsala da yadda za. A gyarata   Kaii NE daga anbayar kadauka ahoto kuyita sharing domin aga aikin Mai gidanka lalle da gyara badan karamiba alamuranka  Muna Kira GA yan media dakuma  Yan siyasarmu da masu kudin..  Hukuma da masu ruwa da tsaki dasu  Ankara agyara wannan matsalar Bamu yarda abamu abinci adaukemu a hotoba saboda zubar da mutuncine Kanawapostnews

Gwamna Yusuf Ya Kaddamar Da Kwamitocin Bincike Kan Karkatar Da Kadarorin Gwamnati Da Rikicin Siyasa A Jihar

Image
Gwamna Yusuf Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da wasu kwamitocin bincike guda biyu da za su bankado almubazzaranci, karkatar da dukiyar al’umma, tayar da rikicin siyasa da kuma bacewar wasu mutane a tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023. A yayin kaddamar da mambobin kwamitocin a ranar Alhamis, Gwamna Yusuf ya sha alwashin gurfanar da duk wanda aka samu yana da hannu kan wannan badakalar. Wani Dansanda Mai Rakiyar Jirgin Kasan Kaduna Zuwa Abuja Ya Rasu Acikin Jirgin Tsohon Shugaban NLC, Ali Ciroma, Ya Rasu A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, gwamnan ya tunatar da cewa, wannan yunkurin na daga cikin alkawarin da ya dauka na kaddamar da bincike tare da hukunta wadanda ke da hannu a rikicin siyasa da aka samu a jihar. Ya ce, “Rikicin siyasa babban koma baya ne ga ci gaban dimokuradiyya a duniya. Yana haifar da asarar rayuka da dukiyoyi tare da rashin aminta da juna daga bangaren al’umma da masu rike da madafun iko. “Bai kam