Tinubu Zai Kaddamar Da Kwamitin Gyaran Mafi Karancin Albashi Ranar Talata
Tinubu Zai Kaddamar Da Kwamitin Gyaran Mafi Karancin Albashi Ranar Talata 6 hours ago Gwamnatin Nijeriya za ta kaddamar da wani kwamiti mai wakilai 37 da zai aiki kan mafi karancin albashin ma’aikata na kasa da bayar da shawarwari kan karin mafi karancin albashi a Nijeriya. Wata sanarwa da daraktan yada labarai na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Segun Imohiosen, ya fitar, ya bayyana cewa kaddamar da kwamitin na cikin umarnin da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar na kafa shi. Ranar Talata aka shirya bikin kaddamar da kwamitin a fadar shugaban kasa da ke Abuja. A cewar sanarwar, Bukar Goni Aji, tsohon shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ne zai shugabanci kwamitin da mambobinsa daga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihohi da kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin kwadago. Sanarwar ta ce, “Daga bangaren Gwamnatin Tarayya, mambobin sun hada da Nkeiruka Onyejeocha da Karamin Ministan Kwadago da Aiki, Hon. Wale Edun da Ministan Kudi.