Dantiye Ya Bukaci Samun Karin Hadin Kai Tsakanin Jami’an Yada Labarai A Kano
- Get link
- X
- Other Apps
Kwamishinan Ma’aikatar yada Labarai na Jihar Kano, Baba Halilu Dantiye, ya bukaci Jami’an yada labarai daga ma’aikatun da Hukumomin Gwamnati da su kara samar da hadin kai da takwarorinsu na Kananan Hukumomi.
Dantiye, ya jadadda muhimmancin hadin guiwa domin yada kyawawan aikace-aikace da tsare-tsaren gwamnati, inda ya bayyana bukatar jami’an yada labaran da su ci gaba da yin aiki tare a lokutan taruka a yankunansu.
- Jariri Ya Yi Batan Dabo A Asibitin Waziri Gidado Da Ke Kano
- Hukumar Hisbah Ta Kaddamar Da Farautar ‘Yan Tiktok 6 A Kano
Kwamishinan ya jinjinawa sadaukar da kan Jami’an yada labaran, ya bayyana dalilin wannan ganawa wadda yace an tsara ta domin ne don tuna masu ayyukansu na sanar da al’umma tare da ankarar da gwamnati kan dukkan wani lamarin da ke bukatar daukin gaggawa domin Inganta rayuwar JJama’arKano.
Kazalika, ya jadadda aniyar ma’aikatar yadda labaran na farfado da mujallar mako-mako da kuma shirinan na gidajen Radio da Talbijin mai taken “Jihar Kano a yau”, Inda ya bukaci karin goyon baya ga Jami’an yada labaran domin kyautata ayyukansu.
Comments