Babban Zauren MDD ya nemi Kwamitin Sulhu ya amince da ƙasar Falasɗinu

 

Babban Zauren MDD ya nemi Kwamitin Sulhu ya amince da ƙasar Falasɗinu


BABAN zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi ƙira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya tabbatar da 'yancin Falasɗinawa ta hanyar amincewa da kasar a matsayin mamba a majalisar.

Falasɗinu dai na da matsayin ƙasa 'yar sa ido tun shekarar 2012, wani abu da ke nuna rashin cikakken 'yancinta na kasancewarta ƙasa mai 'yancin a zauren.

Kwamitin Tsaro na Majalisar ta Dinkin Duniya ne kawai yake da damar tabbatar da hakan.

Amurka za ta hau kujerar naƙi dangane da zaman Falasɗinu samun matsayin zaman cikakkiyar mamba a kwmaitin.

To sai dai zaɓen na ranar Juma'a ya nuna irin goyon bayan da ake nuna wa ƙasar Falasɗinawa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Turai ke ƙoƙarin amincewa da ƙasar Falaɗinawa.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano