Shin me ya sa ƙasashen yammaci ke shakkar manhajar Tiktok?
kasar China ta soki wani kuduri da 'yan majalisar Amurka ke yi wa karatu wanda kuma zai iya kai wa ga haramta amfani da kafar Tiktok a Amurkar, wani abu da Chinar ta bayyana da rashin adalci. Wannan ne dai mataki na baya-bayan a shekarun da kasashen biyu suka kwashe suna zaman tankiya dangane da fargaba kan manhajar wadda wani kamfanin kasar China ya mallaka. Kasashen yammaci da dama dai sun haramtawa jami'ai da 'yan siyasa da jami'an tsaro sauko da manhajar ta Tiktok a na'u'rorin gwamnatocinsu. Shin wadanne dalilai ne ke sa ake shakkar wannan manhaja ta Tiktok? Sannan ta yaya kamfanin ke magance su?. Ga wasu dalilai guda uku. 1. TikTok na karɓar bayanai masu yawa daga abokan hulda TikTok ya ce tsarin karbar bayanai na manhajar na gudana ne bisa yadda ake yi a duniya fasahar sadarwa. Masu suka na yawaita sukar Tiktok da tara bayanai masu yawa. Wani rahoton tsaro na intanet da wasu masu bincike na kamfanin Internet 2.0 na kasar Australia suka wallafa a watan Yuli