Gini mai hawa biyu ya rufta kan magina fiye da 15 a Kano
Ana fargabar wani gini mai hawa biyu da ya ruguje ya faɗa kan wasu magina da ake aikin gini a yankin Kuntau da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano. Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa ginin ya rufta kan magina fiye da 15. Tuni dai masu aikin ceto suka fara zaƙulo mutanen da suka maƙale a ginin. Zuwa lokacin da BBC ta yi magana da majiyarta, an zaƙulo mutum uku sai dai ɗaya a cikinsu ya mutu yayin da biyun ke cikin mawuyacin hali. Kawo yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da ibtila'in ya rutsa da su ba. Article share tools View more share options Share this post Copy this link Karanta karin bayanai kan wannan mashigin