Gini mai hawa biyu ya rufta kan magina fiye da 15 a Kano

 

Gini mai hawa biyu ya rufta kan magina fiye da 15 a Kano

Ana fargabar wani gini mai hawa biyu da ya ruguje ya faɗa kan wasu magina da ake aikin gini a yankin Kuntau da ke ƙaramar hukumar Gwale a jihar Kano.

Wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa ginin ya rufta kan magina fiye da 15.

Tuni dai masu aikin ceto suka fara zaƙulo mutanen da suka maƙale a ginin.

Zuwa lokacin da BBC ta yi magana da majiyarta, an zaƙulo mutum uku sai dai ɗaya a cikinsu ya mutu yayin da biyun ke cikin mawuyacin hali.

Kawo yanzu dai ba a tantance adadin mutanen da ibtila'in ya rutsa da su ba.

Comments

Popular posts from this blog

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga a Neja da Borno

HOTONAN Yadda Kabilar Dakarkari ke cigaba da gudanar da wasannin al'adun Gargajiya Zuru Uhola.

Babban Zauren MDD ya nemi Kwamitin Sulhu ya amince da ƙasar Falasɗinu