Posts

Showing posts from March 10, 2024

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Image
Kasar Saudiyya ta bayar da sanarwar ganin watan Azumin Ramadana. Shafin X na Masallatan Harami biyu masu daraja ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa. Ganin watan ya sa gobe Litinin za ta zama 1 ga watan Ramadan na shekarar 1445, wanda ya zo daidai da 11 ga watan Maris ɗin 2024. Hukumar Masallatan ta sanar da cewa a daren yau ne za a fara gabatar da Sallar Asham, inda Sheikh Sudais da Sheikh Badr Al Turki da kuma Al Waleed Al Shamsaan za su jagorance ta a Masallacin Harami na Makkah, yayin da Sheikh Muhammad Barhaji da Abdul Muhsin Al Qasim za su jagoranci sallar a Masallacin Manzon Allah SAW na Madina.

Tinubu ya umarci Kwastam ta mayar da kayan abincin da ta kwace wa mutane

Image
Babban Kwanturan Hukumar Kwastam ta Najeriya, Bashir Adewale Adeniyi ya ce shugaban ƙasar Bola Tinubu ya umarci hukumar ta mayar da duka abinci dangin tsaba da ta ƙwace daga wajen mutane domin sayar da su a kasuwanni. Cikin wata sanarwa da hukumar Kwastam ɗin ta fitar a shafinta na X, ta ce mista Adeniyi ya bayyana hakan ne lokacin wata ziyara da ya kai kan iyakar Kwangwalam da ke ƙaramar hukumar Maiadua a jihar Katsina inda ya gana da masu ruwa da tsaki. Shugaban Kwastam ɗin ya ce umarnin shugaba Tinubun wata alama ce da ke nuna burin shugaban ƙasar na tabbatar da al'ummar ƙasar sun wadata da abinci ta yadda farashinsa zai sauka a kasuwannin ƙasar. Ya ƙara da cewa sharaɗin mayar da kayan abincin hannun mutanen da aka ƙwace musun, shi ne za su sayar da shi a kasuwannin Najeriya. Mista Adeniyi ya kuma ce dole ne a samu dangantakar alaƙa tsakanin jami'an tsaro da ci gaban tattalin arziki, yana mai cewa idan babu zaman lafiya da tsaro kasuwanci ba zai inganta ba.