Dalilin da ya sa hukumar Alhazan Najeriya ta ƙara kusan naira miliyan biyu
Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ƙara kuɗin kujerar aikin Hajji da miliyan ɗaya da dubu ɗari tara, inda yanzu kuɗin suka koma naira miliyan shida da dubu 800 kan kujera ɗaya. Hukumar ta ce hakan ya faru ne sakamakon tashin farashin dala wadda da ita ce ake yin kiyasin dukkanin abubuwan da maniyyata suke bukata. Mai magana da yawun hukumar, Fatima Sanda Usara ta ce wadanda ba su fara biyan wani abu daga cikin kudin kujerar ba za su biya naira miliyan takwas, saboda lokacin da aka fitar da farashin kujerar aikin Hajjin bana dala ba ta yi tashin da ta yi ba yanzu. Hukumar ta kuma ba maniyyata aikin Hajjin na bana wa'adin zuwa 29 ga watan nan na Maris da ake ciki domin kammala biyan kudin: " Wadanda suka kasa biya suna da zaɓi biyu ko dai su rubuta a mayar masu da kuɗinsu ko kuma su ajiye kudin har zuwa shekara mai zuwa." Hukumar ta ce mutum 49,000 ne suka biya kudin kujerun a farashin baya daga cikin kujeru 75,000 da Saudiya ta ba mahajjan gwamnati yayin da ƴan kas...