Matsalar hare-haren ƴan bindiga ta ɗauki sabon salo a jihar Zamfara
A Najeriya, hare-haren da ƴan bindiga ke kaiwa garuruwa da ƙauyuka a jihar Zamfara ya ɗauki sabon salo, sakamakon yadda suka fara mayar da hankali ga yi wa matan aure fyaɗe a gidajen mazajensu da aikata kisan gilla, da dai sauran ayyukan ta'asa a garin Kalgon Ƙunci na yankin karamar hukumar Tsafe.
Lamarin ya sa kashi kimanin saba'in cikin ɗari na jama’ar garin sun tsare zuwa wasu wurare.
Yayin da jama'a suka sabunta kyakkyawan fatan samun saukin matsalar tsaro, bayan ƙaddamar da rundunar kare fararen hula a jihar Zamfara, ƴan bindiga sun sauya wa gyambo kafa, a garin Kuncin Kalgo na yammacin yankin karamar hukumar Tsafe. Kamar yadda wani mutumin garin da ya bukaci a sakaya sunansa, ya shaida wa BBC:
‘‘A da dai za su shigo cikin garin mu, su wulaƙanta mu, su saci dabbobi, su yi garkuwa da mutane. To yanzu da ranar Allah za su shigo garin mu, kuma ba su fita sai ƙarfe sha biyu da dare, da makaman su tunda mutum ɗaya za ka ga ya rungume bindiga biyu ya rataya, da khaki. Wallahi an kai matakin da za su shiga duk gidan da suke so, su yi amfani da matan gidan, su fita kuma duk macen da ta ƙi biyayya ga buƙatar su sai su tafi da ita daji su yi yadda suke so, kwana biyu, kwana uku, kwana huɗu, sannan su dawo da ita’’
Mutumin na garin Kuncin Kalgo ya ce, munin al'amarin bai tsaya a nan ba: ‘‘Sama da shekara 10 da ta wuce ba mu da ɗan sanda guda 1 a cikin Kuncin Kalgo, shiyasa suke mana wulakanci. Mu dai waɗannan mutane ƙarƙashin su muke, su ke mulkin mu. Da kaka mutanen nan suka zo suka ce mu haɗa masu kuɗi naira miliyan 15, kan za su bari mu cire abin da muka noma. Sai da aka bi gida-gida aka haɗa wannan kuɗi aka kai wa mutanen nan, amma bayan kwana uku da basu kuɗin sai suka ce bamu isa mu cire amfanin gonar ba, suka sa wuta suka ƙona shi.’’
Jama’ar kunchin Kalgo sun ce sun koka ga hukumomin duk da suka kamata, amma har yanzu ba su sami dauki ba. Wannan ne ya ma tilasta wa mafi yawancinsu yin gudun hijira, a cewar mutumin garin:
‘‘Duk mutanen da suke da wani waje da za su tafi sun kwashe kayan su sun tafi. Kullum mutanen suna barin kunchin Kalgo ne’’
Gwamnatin jihar Zamfara dai tana sane da wannan ƙunci da jama'ar garin Kuncin Kalgo ke ciki, kuma ta ce tana bin matakin da ya kamata don magance matsalar, in ji Sulaiman Bala Idris, mai magana da yawun gwamnan jihar:
‘‘To wannan abu da ke faruwa, abu ne abin takaici kuma gwamnati na nan tana ɗaukar matakan da suka dace domin kawo ƙarshen lamarin. Ba ma nan kaɗai ba, muna bada tabbacin za a kawo ƙarshen wannan lamari da yardar Allah.
Comments