Shugabannin duniya na alhinin rasuwar Navalny
Shugabannin ƙasashen duniya na ci gaba da alhinin rasuwar jagoran adawar Rasha Alexei Navalvy.
Mista Navalny ya rasu ne a ɗaya daga cikin gidajen yari mafiya tsaro a ƙasar, inda yake zaman hukuncin da aka yanke masa.
Shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, ya ce ga alamu jagoran adawar Rashan ya rasa ransa ne saboda jarumtakarsa.
Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak, ya ce Mista Navalny ya kasance na gaba wajen hanƙoron kawo da Dimokradiyya a Rasha.
Cikin wata sanarwar hadin gwiwa, shugabannin ƙasashen kungiyar tarayyar Turai sun ce sannu a hankali gwamnatin Putin ta kashe Mr Navalny.
Hukumar kare hakkin ɗan'dam ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta kaɗu da samun labarin mutuwarsa, ta na mai cewa idan har mutum ya mutu a lokacin da ake tsare da shi to ana danganta mutuwar tasa da laifin gwamnatin ƙasar da yake tsaren.
Comments