shi a ranar 8 ga watan Agusta, 2021, bayan


 shi a ranar 8 ga watan Agusta, 2021, bayan ya maye gurbin Eshaq Jahangiri, wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban ƙasar Hassan Rouhani na farko.

A cikin watan Yulin 2010, Tarayyar Turai ta saka Mohamed Mokhber a cikin jerin sunayen jami'an gwamnati da ta kakaba wa takunkumi tare da zarginsa da hannu a "ayyukan makami mai linzami na nukiliya", kuma bayan shekaru biyu ya cire sunansa daga jerin.

An kuma sanya shi a cikin jerin takunkumin da ma'aikatar baitulmali ta Amurka ta a watan Janairun 2021. Washington ta fada a cikin jerin sunayen cewa kwamitin "yana da ruwa da tsaki a kusan kowane bangare na tattalin arzikin Iran, ciki har da makamashi da sadarwa da kuma sabis na kudi."

Ya kasance na kusa da shugaban Iran Ebrahim Raisi, kuma ya kasance mai bin diddigin batutuwan cikin gida da dama. Ya ziyarci ƙasashe da dama tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da suka gabata.

Mokhbar ya kuma kasance babban jami'i a cikin kungiyoyin kasuwanci da jagoran juyin juya halin Musulunci Ali Khamenei ke kula da shi, da kuma cibiyar sadarwar "Iran International" ta bayyana shi a matsayin "ƙwarare ta fannin tattalin arziki."

Ya wallafa littattafan tattalin arziki da dama wadanda suka haɗa da:

Manyan masana tattalin arziki na duniya - da ya fitar a shekarar 2013.

Hanyar Ci Gaban Tattalin Arziki da Adalci - da ya fitar a shekarar 2015.

Haɓaka tattalin arziƙi a Iran - da ya fitar a shekarar 2016.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano