Ƙungiyar Tarayyar Afirka ta haramta safarar fatar jaki...


...

Ƙungiyoyin ba da agaji ga dabbobi sun yi maraba da dokar haramta safarar fatar jaki da aka kafa a faɗin Afirka.

Wannan dokar dai ya haramta yanka jakai a ƙasashe 55 na Afrika.

Shugabannin kasashen Afirka sun amince da haramcin ne a karshen taron kungiyar Tarayyar Afirka da aka kammala a kasar Habasha ranar Lahadi.

Dr Onyango ya shaida wa BBC cewa haramcin zai kare jakai da kuma rayuwar miliyoyin da suka dogara da su.

Buƙatar fatar jakan dai na da nasaba da shaharar wani maganin gargajiya da ake yi da fatar jaki me suna Ejiao a ƙasar China.

Wasu sun yi imanin Ejiao yana da fa'idodin hana tsufa da kuma lafiyar jiki, kodayake wannan ba shi da tabbas.

Wata ƙungiyar agaji mai suna 'The donkey sactuary ta kira wannan sana’ar na saye da sayaa da fatar jaki a matsayin “mummuna da rashin dorewa” inda ta ce sana'ar ta yi sanadin raguwar jakai a faɗin duniya musamman a kasashen Afirka da Kudancin Amurka.

Kimanin kashi biyu bisa uku na adadin jakai miliyan 53 na duniya ana kiyasin suna Afirka ne.

Ana kallon haramcin a matsayin wani muhimmin mataki na kiyaye wadannan dabbobi da kuma tallafawa al'ummomin karkara da suka dogara da su don jigilar kayayyaki da kuma ayyukansu na yau da kullum.

Comments

Popular posts from this blog

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano

gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake nada amb Yusuf imam ogan ɓoye