Ko kun san ƙwaƙular kunne na haifar da matsalar ji?

Kwakular kunne


Kunne wani ɓangare ne mai muhimmanci a jikin ɗan’adam wanda ya kamata a kula da shi.

Kunnuwanmu na da mahimmanci ga lafiyarmu - amma duk da haka, galibi ba mu kula yadda ya kamata.

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ware ranar uku ga watan Maris a matsayin "ranar ji ta duniya" don fadakar da al’umma muhimmancin kula da jinsu.

Taken bikin ranar ta bana shi ne “sauya tunanin mutane game da matsalar ji” - domin an gano akwai wani tunanin da mutane suke da shi wanda ke kara haifar da matsala ga jinsu.

Wata kididdiga ta Hukumar lafiya ta duniya ta nuna cewa aƙalla mutum miliyan 430 ne a fadin duniya ke fama da matsalar da ta shafi rashin ji, inda kuma a Najeriya fiye da mutum miliyan 20 ke fama da wannan matsalar.

Alƙalumman sun nuna cewa yawan mutanen da ke da matsalar ji a duniya yana karuwa kusan kullum.

Kuma masana sun ce galibi mutane ne ke yi wa kunnuwansu illa ba tare da sun sani ba ta hanyar bin wasu hanyoyi da ba su dace ba musamman ƙoƙarin cire dattin kunne ko idan sun ji sauyi ko ƙaiƙayi a kunnen.

Bisa shawarar likita, kada ka taɓa koƙarin tsaftace cikin kunnenka ta hanyar amfani da auduga ko yatsa ko cusa wani abu - domin yana da hatsarin haifar da matsalolin ji ko ma fasa dodon kunne.

Shin akwai dattin kunne?

Galibin mutane kan yi amfani da wasu abubuwa da nufin cire dattin kunne.

Ana amfani da audugar kunne da murfin biro da karen ashana ko tsintiya wajen cire dattin kunne.

Amma a cewar Dr Mustapha Sa’idu kwararren likitan kunne da hanci da kuma maƙogaro a asibitin Murtala da ke Kano a Najeriya, Allah ya halicci kunne ne yadda zai dinga goge kansa da kansa saboda haka ba a bukatar mutum ya riƙa saka wasu abubuwa da nufin cire dattin kunne.

Ya ce kunne yana da wani maiƙo wanda ke halittar kansa da ke taimakawa lafiyar kunnen.

“Abin da ake gani kamar datti idan an saka auduga ko wani tsinke –maiko ne ba datti ba ne wanda ke ba da kariya ga kunne da ke kare datti da hana ƙura zuwa ga dodon kunne.”

"Maiƙon yana sa kunnen yin dadi. Kunne yakan yi ƙaiƙayiyi saboda wata kwayar cuta amma kuskure ne saka wani abu a kunne da nufin cire datti," in ji likitan.

Likitan ya ce ƙoƙarin cire maiƙon a lokacin da yake aikinsa na ƙara lafiyar kunnen zai iya haifar da matsala.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano