EFCC na bincike kan yarjejeniyar Nigeria Air - Keyamo
Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Festur Keyamo ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC na gudanar da bincike kan yarjejeniyar kamfanin jiragen sama na ƙasar wato 'Nagerian Air' mai cike da ce-ce-ku-ce da gwamnatin tarayya ta ƙulla ƙarƙashin tsohon ministan kula da sufurin jiragen sama na ƙasar Hadi Sirika
Yayin da yake zantawa da gidan talbijin na Channels ranar Laraba, mista Keyamo ya ce “EFCC na bincike kan yarjejeniyar.
''Ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma muna jiran rahoton binciken''.
Mista Keyamo wanda suka yi aiki tare da Siriki a matsayin ministocin gwamnatin Buhari, ya ce babu wani kamfanin jirage da ke aiki a matsayin kamfanin jirage na ƙasa, amma ya ce za a samar da nagartaccen kamfanin jirage na ƙasa.
A watan Agustan bara ne Mista Keyamo ya ƙaryata yarjejeniyar da Sirika ya ƙulla tare da dakatar da duk wani shiri da ke cikin yarjejeniyar.
Batun yarjejeniyar kamfanin 'Nigerian Air' dai ya ja hankalin 'yan ƙasar ne bayan da jirgin kamfanin ya yi ɓatan-dabo jim kaɗan bayan ƙaddamar da shi, kwanaki kafin ƙarewar wa'adin gwamnatin tsohon shugaban ƙasar Muhamdu Buhari.
Ce-ce-ku-cen da ke tattare da yarjajeniyar kamfanin Nigerian Air ya tilasta wa shugaban kamfanin Ethiopian Airlines, Girma Wake ajiye muƙaminsa.
Manajan daraktan kamfanin Najerian Air, Capt Dapo Olumide, ya ce jirgin da aka gabatar a lokacin ƙaddamar da kamfanin, na Ethiopian Airlines ne.
Inda ya ƙara da cewa a ranar da wa'adin mulkin shugaba Buhari ya ƙare cikin watan Mayu, aka mayar wa Ethiopian Airlines jirgin bayan ƙaddamarwar.
Tuni dai dama majalisun dokokin ƙasar biyu suka bayyana ƙaddamar da kamfanin 'Nigerian Air' da aka yi a matsayin yaudara
Comments