Muna tsare da shugabannin Binance a Najeriya'

..

ASALIN HOTON,ALAMY

Gwamnatin Najeriya ta tabbatar wa BBC cewar tana tsare da wasu manyan jami'an shafin hada-hadar kuɗin kirifto na Binance a birnin Abuja.

Hakan na zuwa ne bayan wasu rahotanni da suka ɓulla a daren ranar Laraba da ke nuna cewa hukumomi na tsare da jami'an.

A wata tattaunawa da BBC, Zakari Mijinyawa, wanda shi ne shugaban sashen yaɗa labaru na ofishin mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkokin tsaro, ya ce "ana yi wa jami'an tamnayoyi ne ƙarƙashin binciken da hukumomin tsaro ke yi kan daidata kasuwar musayar kuɗi, wanda ofishin na mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ke jagoranta".

Hukumomi na zargin shafin na Binance ne da laifin "ƙayyade farashin kuɗin ƙasashen waje a ƙasar".

Darajar takardar kuɗin Najeriya dai ta yi faduwar da ba a taɓa gani ba a tarihi tun bayan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya ƙyale kasuwa ta tantance darajarta.

Lamarin ya ƙara jefa tattalin arziƙin Najeriya da kuma al'umma ƙasar cikin garari, abun da ake ganin ya samo asali daga cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi.

Zakari Mijinyawa ya shaida wa BBC cewa "yanzu haka akwai tattaunawa da kuma yarjejenyoyi da ake yi da jami'an na Binance, kuma suna bayar da haɗin kai."

Sai dai jami'in bai yi wa BBC cikakken bayani kan tsawon lokacin da za a ɗauka ana binciken, ko kuma yarjejeniyar da ake son ƙullawa ba tsakanin gwamnati da shafin na Binance

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano