Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina

 ‘Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina


Rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Faskari da Malumfashi a jihar, a ranakun 8 da 9 ga watan Mayun 2024.


Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce ‘yan bindigar sun kai harin farko ne a ranar 8 ga watan Mayu, 2024, bayan sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau, a kauyen Unguwar Boka, a karamar hukumar Faskari.


A cewarsa, ‘yan ta’ad-dan sun far wa fasinjojin da ke tafiya a cikin wata kirar motar Golf III, inda suka ci da halbe-halbe.


Sai dai Sadiq ya bayyana cewa shirin nasu ya ci tura sakamakon wani dauki da jami’an sintiri suka kai.


Daily news hausa

Comments