Kumbon da China ya sauka a kudancin duniyar wata
Kafofin yada labaran China sun ce wani kumbon da aka harba zuwa duniyar wata ya sauka a ɓangaren watan da ba a taba zuwa ba kuma zai debo samfuran duwatsu da za a gudanar da bincike a kansu.
Kumbon mara matuƙi mai suna 'Chang'e 6' wadda aka harba a farkon watan Mayu, ya sauka a wani yankı da ke ɓangaren kudancin duniyar wata.
Masana kimiyya na farin ciki da matakin saboda a cewarsu za su samu damar nazarin waɗannan duwatsun da babu wanda ya taɓa ganin irinsu
Comments