Al'umma na gudun hijira a Zamfara Ƴan gudun hijira A
Matsalar hare-haren 'yan bindiga da ta addabi al'ummar garin Jangebe da wasu kauyukansa akalla biyar, a yankin karamar hukumar Talatar Mafara ta jihar Zamfara, ta kara kwabewa.
A cewar wani mutumin yankin da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce tun daga ranar talata har zuwa laraba, kauyukan Jangebe biyar zuwa shida suna cikin iftila’in kashe-kashe.
Mazaunin na Jangebe ya shaida wa BBC cewa a baya an samu saukin lamarin, sai dai kwanan nan abin ya dawo sabo a yankin Talatar Mafara ta Kudu, kuma yawacin mutanen kauyukan yankin, “Muna rokon gwamnatin tarayya da ta jiha su kawo mana dauki.”
A garin Magazu na yankin karamar hukumar Tsafe ma, hare-haren 'yan bindigan suna kara munana, kamar yadda wani mutumin garin da ba ya so a fadi sunansa ya bayyana wa BBC.
“A baya an samu saukin lamarin sosai, sai dai yanzu abin ya dawo fiye da yadda ake tsammani, ko ranar Laraba sun shiga garin Magazu sun kwashi matan aure, mata da magidanta na ta barin gari domin yin gudun hijira."
Mutumin ya kuma shaida wa BBC cewa ko a farkon watan ramadan yanbindigar sun shiga sun dauki mata gida-gida sai da aka bada miliyan hudu da dubu 300, "bayan an kai masu suka kuma nemi a saya masu mashin, kuma bayan sun sauko matan da kwana biyu suka sake dawowa suka kwashi mutane."
Comments