Yau take sallah barka da sallah










Ya ce ƙwarewarsu da rashin bai wa abokan kulɗa kunya wajen shirya abincin fita-kunya kamar tuwon sallah cikin gwaninta sun sa mutane na ƙara neman ƙwararrun masu dafa abinci.

Ko ba komai, in ji shi, ba a ko'ina ake samun ɗanɗano da daɗi da iya tsara dafaffen abinci mai rai da lafiya a kwano, da ƙamshin burgewa ba.

"A kawo muku har gida, ba tare da kun san wata wahalar da aka yi ba, kawai ci kuka sani" in ji mai gidan abincin.

"Sai dai ku ci, ku ji daɗi, shi ma wanda aka ba, ya ci ya ji daɗi. Sai a yi ta tunanin ta yaya aka yi haka?"

Mata da yawa kamar Ni'ima Ibrahim, ba lallai su yarda da wannan ra'ayi ba.

Suna ganin duk da zamani, amma girki ya fi yarda da hannun mata.

Hatta naƙaltar yadda ake shirya tuwon sallah, ba abu ne da ke buƙatar wuta-wuta da riƙon maza ba.

Gwanintar mata ta fi tashi a girkin tuwon sallah

Mata suna bai wa girkin tuwon sallah wata kulawa ta musamman, cewar Dr Hadiza Koko. "Mace du wadda take, in aka ce tuwon sallah za ta yi. Dole ta aje hankalinta ta tabbatar da tuwon nan ya yi daɗi.

Saboda tuwo ya yi laushi kamar yadda ake buƙata, sai an jiƙa shinkafa ta kwana a ruwa, in ji Ni'ima Ibrahim.

"Kuma sauran cefane kamar su kabewa, su alayyahu da tantaƙwashi ya fi a yi shi ana gobe sallar nan, saboda ka samu komai irin (ɗanye) sharr daga gona gwanin kyau.

Ta ce saboda miyar sallah ta yi ƙamshi da ɗanɗanon ci-manta-hularka, ba ta sa nama nau'i ɗaya.

Maimakon haka takan tanadi tantaƙwashi da kajin Hausa.

"Za ka ga irin ya ɗan faffashe haka. E, don kaji ake sa wa sosai, irin duk lomar da za a yi, a ji an haɗo da kaza," in ji uwargidan.

Dr Hadiza Koko ta ce al'adar ɗebiya ko kuma ba-ni-in-ba-ka kaɗai da ake yi wa tuwon sallah, tana sa ko a gida aka yi abincin a samu wadatarsa.

"Saboda a samu, wannan ranat, ka ci abinci kala-kala. Don in wanda kad dahwa kai kaɗai, yana yiwuwa ma, ba ka so nai".

Ƙwararriyar ta ce abinci ne da bai cika sa taiɓa ba. Saboda cin rana ɗaya ne a shekara.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano