Mahaifiyata abar alfarina

 Mahaifiya abar alfarina

"Ana cewa kafin ka auri mace ka dubi wace ce mahaifiyarta, don akwai tsammani nason ɗabi'a, shawara ce mai kyau. Idan tana zaune da kishiya, ya mu'amalarsu take? Wacce irin kuɗuba take yi wa 'ya'yanta? Idan akwai yayar yarinya da ta yi aure, ya 'interferance' na mahaifiyyar yake a gidan auren 'ya'yanta... ka duba wannan, ba iya soyayya ba.


Ita ma mace! Yana da kyau ke ma ki duba alaƙar namiji da 'yan mahaifiyyarsa da 'yan uwansa mata. A zahiri a aikace, me ya ɗauki mace? 'Yar tsana (toy) ko mutum? Yana tausayinsu? Yana taimaka musu? Wannan ɗabi'a zai 


Ku rabu da gigi da giyar soyayyar mai bugarwa, a marhalar soyayya kowa 'perfection' nasa yake ƙoƙarin nunawa don ya samu karɓuwa, tare da ƙoƙarin lulluɓe naƙasunsa a halayya da ɗabi'a, saboda a marhalar nema ana tsayuwa ne na ɗan lokaci. Halayya kuma ba ta ɓoyewa, saboda ita ce ke sarrafa gaɓɓan jikinmu sai hali ya bayyana komai tsawon lokacin zama na dindindin.


Da yake Ubangiji shi ne Masanin fili da zahiri "عليم بذات الصدور", shi ba a ɓoye masa hatta abin dake cikin zukata, idan ka yi addu'ar alheri, kuma babu alheri a tattare da mutum sai ya kawo sanadi ya haɗa. Idan kuma akwai alheri, sai ya kawo sanadi ya haɗa. KADA A YI WASA DA ADDU'A".

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano