Dambarwar Bashi Ta Dumama Jihar Kaduna

Dambarwar Bashi Ta Dumama Jihar Kaduna

Biyo bayan kalaman da Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya yi na cewa, ya gaji bashin miliyoyin Dala da biliyoyin Naira daga gwamnatin Nasir el-Rufai da ya karbi ragama a hannunta; fagen siyasar jihar na ci gaba dumama sakamakon kurar da ke tashi.

A yayin gudanar da wani taro da al’ummar jiha kwanan nan a zauren taro na Umaru Musa ‘Yar’Adua da ke Dandalin Murtala Sikwaya, Uba Sani, ya ce ya gaji bashin da kimanin Dala miliyan 587 da Naira biliyan 85 da kuma tarin ayyukan da ba a kammala ba daga Gwamnatin Nasir el-Rufai. Sai kuma ayyuka 115 wanda ‘yan kwangila ba su kammala ba

Haka zalika, Uba Sani ya ce sakamakon dimbin bashin, hatta albashin ma’aikata ba zai iya biya ba. Kodayake, tuni ya kai kukansa wurin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, kan yadda zai taimaka masa wajen warware wannan matsala, amma sai shugaban kasar ya bayyana masa cewa; shi ma abin ya fi karfinsa, sakamakon an ciyo bashin ne daga Bankin Duniya.

Haka kuma Gwamna Sani ya koka kan yadda farashin canji ya tashi, wanda ya sa yanzu Jihar Kaduna na biyan kusan ninki uku na bashin.

Ya bayyana cewa an cire naira biliyan 7 daga cikin biliyan 10 da gwamnatin tarayya ta ware wa jihar a watan Maris sakamakon biyan bashi.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano