Mun yi maganin masu bai wa ƴan bindiga bayanai-Gwamna Dikko Radda
Gwamnan jihar Katsina ya yi kira ga jama’ar jihar su tallafawa jami’an tsaro wajen yaƙi da ƴan bindiga da suka addabi sassan jihar.
Gwamnan Umaru Dikko Radda ya ce akwai buƙatar mutane, musamman matasa su haɗa kansu domin tallafawa jami’an tsaro wajen aikin kawar da matsalar tsaron.
A hirar sa da BBC, gwamnan ya kuma musanta rahotannin da ke cewa gwamnatinsa ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma yayin da ƴan bindiga ke cigaba da kai hare hare a wasu yankunan jihar.
Gwamnan ya ce tun bayan da ya karɓi mulki, gwamnatinsa ta samu nasara sosai a yakin da take yi da ƴan bindiga, ciki har da kafuwar rundunar tsaro ta musaman wadda a cewarsa ta taimaka wajan dakile hare haren yan bindigar.
Ya ce: "Mutumin Jibia da mutumin Batsari da na Kankara da na Danmusa da na Sabuwa da na Faskari da na Dandume sun san cewa an samu sauƙi a matsalar tsaron da muke fuskanta a jihar Katsina’’
Ya yi bayanin cewa sabbin dabarun da gwamnati ta ɓullo da su sun taimaka sosai wajen kawar da masu bai wa ƴan bindigar bayanan sirri, waɗanda da ma can masana a fannin tsaro ke cewa su ne babbar illa a yaƙi da masu garkuwa da mutane.
"Yanzu irin waɗannan informants ɗin da ke zuwa suna basu labarin in za su shigo su tai gidan wane ko wane an yi maganin su. Yanzu sai dai su shigo a kurumce su kwashe wanda za su kwasa kawai don a san suna nan’’
Gwamnan ya ce an kama mutane da dama masu bayar da bayanan sirri ga ƴan bindigar kuma bincike ya tabbatar cewa suna da hannu dumu-dumu a wannan ɗanyen aiki.
Dangane da tsadar rayuwa da ake fama da ita a Najeriya kuwa, gwamna Radda ya ce gwamnatinsa ta yi taron masu ruwa da tsaki, kuma za ta fitar da hanyoyin kawo sauki ga al’ummar jihar nan ba da jimawa ba.
Comments