Dalilin mu na maka gwamnonin Najeriya a kotu- SERAP
Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta yi ƙarin haske akan dalilan kai ƙarar gwamnonin ƙasar 36 da kuma ministan birnin tarayyar Abuja gaban kotu.
Kungiyar ta ce ta shigar da wannan kara ne saboda rashin bayar da bayanai kan yadda gwamnonin jihohin Najeriya 36 da ministan Abuja, suka kashe kuɗaɗen da suka ciyo na bashin naira tiriliyan kusan shida, da kuma sama da dala billiyan 4 da rabi, ba tare da bahasi ba.
SERAP ta buƙaci kotun da ta gayyaci hukumar EFCC da ICPC domin ƙaddamar da bincike kan yadda aka kashe basusukan da gwamnonin suka karɓo.
Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce ta shigar da karar ne a ranar juma'ar makon da ya gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja.
SERAP din ta ce, ta shigar da karar ne bayan gazawar gwamnonin wajen yi wa al'ummar su bayanin yadda suka kashe basusukan da suka karɓo da wajen da aka aiwatar da auikin da aka karbo bashin dominsu.
Kolawole Oluwadare mataimakin daraktan kungiyar ta SERAP ya yi karin bayani:
Ya ce: ’’Mun je kotu ne don a tursasa, tare da bai wa gwamnonin da ministan birnin Abuja umarnin bayar da bayani na yarjejeniyar da suka cimma da waɗanda suka basu bashin. Sannan mun buƙaci a gayyato hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC, da hukumar yaƙi da masu yiwa tattali arzikin ƙasa ta’annati ta ICPC domin su ƙaddamar da bincike kan yadda aka ciwo bashin. Yan Najeriya musamman na jihohin da aka ciwo bashin na da haƙƙin sanin yadda aka yi da kuɗaɗen, da yadda aka kashe su, da inda aka kashe su. Saboda haka bayyana irin waɗannan bayanai haƙƙi ne a kan masu mulki.’’
Comments