Posts

Showing posts from 2024

FBI ta bayyana sunan mutumin da ya yi yunƙurin kashe Trump

Image
  FBI ta bayyana sunan mutumin da ya yi yunƙurin kashe Trump ASALIN HOTO Hukumar tsaro ta FBI ta bayyana sunan mutumin da ake zargi da yunƙurin kashe tsohon shugaban Amurka Donald Trump a wajen yaƙin neman zaɓe. Hukumar ta ce sunan mutumin Thomas Matthew Crooks, kuma ɗan asalin yankin Bethel park ne a Pennysylvania. FBI ta ce tana binciken lamarin a matsayin yunƙurin kisan kai, kuma ba zata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kammala bincike. Hukumar ƴan sandan Pennsylvania ta ce hankali ya kwanta a yankin domin kuwa babu sauran barazanar aikata wani laifin mai kama da wannan. Hukumar leƙen asirin Amurka ta ce ''an harbe mutanen da ake zargi da kai harin kuma ya mutu nan take,'' kamar yadda mai magana da yawun hukumar Anthony Guglielmi ya tabbatar. Ya ƙara da cewa akwai wani ɗan kallo da aka kashe a wajen, yayin da wasu mutane biyu suka samu rauni. FBI ta ce mutumin da ake zargin ba ya ɗauke da wata shaida mai bayani a kansa, amma za a gudanar da gwajin ƙwayar halitta domin gano c...

Shugabannin duniya sun bayyana alhini kan harin da aka kai wa Trump

Image
  Shugabannin duniya sun bayyana alhini kan harin da aka kai wa Trump Shugabannin duniya sun bayyana alhini kan harin da aka kai wa Trump ASALIN HOTON, AP Shugabannin ƙasashen duniya sun mayar da martani da kaɗuwa dangane da harin da aka kai wa Donald Trump. Firaiministan Burtaniya, Keir Starmer, ya ce ya yi matukar kaɗuwa da labarin harin. Takwaransa na Hungary Viktor Orban wanda ya ziyarci Mista Trump kwanan nan, ya ce yana sanya shi a addu'a, yayin da Narendra Modi na Indiya ya ce tashin hankali ba shi da gurbi a tsarin dimokuradiyya. Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, ya ce ya yi mamakin faruwar lamarin, to amma yana masa fatan samun lafiya. Shugaban Argentina, Javier Milei, ya nuna fushinsa, inda ya zargi masu sasaucin ra'ayi da rungumar ta'addanci, maimakon tafarkin dimukradiyya

Kumbon da China ya sauka a kudancin duniyar wata

Image
  ASALIN HOT Bayanan hoto, A farkon watan mayu ne aka harba kumbon mai suna 'Chang'e 6' Kafofin yada labaran China sun ce wani kumbon da aka harba zuwa duniyar wata ya sauka a ɓangaren watan da ba a taba zuwa ba kuma zai debo samfuran duwatsu da za a gudanar da bincike a kansu. Kumbon mara matuƙi mai suna 'Chang'e 6' wadda aka harba a farkon watan Mayu, ya sauka a wani yankı da ke ɓangaren kudancin duniyar wata. Masana kimiyya na farin ciki da matakin saboda a cewarsu za su samu damar nazarin waɗannan duwatsun da babu wanda ya taɓa ganin irinsu

Shugaba Bola Tinubu ya amince da fara amfani da sabon taken Najeriya, wanda

Image
 Shugaba Bola Tinubu ya amince da fara amfani da sabon taken Najeriya, wanda shi ne taken ƙasar na farko kafin sauya shi zuwa wanda aka fi sani a yanzu.  Shin kun iya rera taken? 📸 BBC Hausa

Puskas Arena zai karbi wasan karshe a Champions League 2026

Image
  ASALIN H Sa'o'i 2 da suka wuce Za a buga wasan karshe a Champions League a 2026 a Budapest a filin da ake kira Puskas Arena, inji Uefa ranar Laraba, bayan tashi daga babban taron da ta gudanar a Dublin. Filin dake cin ƴan kallo 67,215 shine wajen da tawagar Hungary ke buga wasanni, wanda ya karbi bakuncin wasa hudu a Euro 2020 da na karshe a Europa League tsakanin Sevilla da Roma. An ɗage taron zabar filin da zai shirya wasan karshe a 2027 zuwa watan Satumba, bayan da Uefa ke son jin karin bayani kan shirin gyaran San Siro, inda AC Milan da Inter ke wasanni. Haka kuma Uefa ta sanar da cewar za a buga wasan karshe a Champions League na mata a 2026 a Norway, Ullevaal Stadion. Shi kuwa filin wasa na Besiktas Park a Turkiya, zai shirya karawar karshe a Europa League a 2026 da kuma Europa Conference League a 2027. Jamus za ta karbi bakuncin wasa biyu - Filin wasa na Frankfurk zai shirya wasan karshe a Europa League a 2027 da kuma Europa Conference League a 2026 a filin RB Leipzig ...

shi a ranar 8 ga watan Agusta, 2021, bayan

Image
  shi a ranar 8 ga watan Agusta, 2021, bayan ya maye gurbin Eshaq Jahangiri, wanda shi ne tsohon mataimakin shugaban ƙasar Hassan Rouhani na farko. A cikin watan Yulin 2010, Tarayyar Turai ta saka Mohamed Mokhber a cikin jerin sunayen jami'an gwamnati da ta kakaba wa takunkumi tare da zarginsa da hannu a "ayyukan makami mai linzami na nukiliya", kuma bayan shekaru biyu ya cire sunansa daga jerin. An kuma sanya shi a cikin jerin takunkumin da ma'aikatar baitulmali ta Amurka ta a watan Janairun 2021. Washington ta fada a cikin jerin sunayen cewa kwamitin "yana da ruwa da tsaki a kusan kowane bangare na tattalin arzikin Iran, ciki har da makamashi da sadarwa da kuma sabis na kudi." Ya kasance na kusa da shugaban Iran Ebrahim Raisi, kuma ya kasance mai bin diddigin batutuwan cikin gida da dama. Ya ziyarci ƙasashe da dama tare da sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa a fannoni daban-daban cikin shekaru biyu da suka gabata. Mokhbar ya kuma kasance babban jami...

Malam magana ake ta matasa a yau lokaci yayi dole mufito muba mara da kunya

 Malam magana ake ta matasa a yau lokaci yayi dole mufito muba mara da kunya 

Halin da makarantar firamare ta garin Bargi ke ciki a karamar hukumar Kiru.

Image
Halin da makarantar firamare ta garin Bargi ke ciki a karamar hukumar Kiru. Shekaru biyu bayan rahoton Premier Radio kan mummunan halin da makaranta ke ciki har yanzu ba abinda ya sauya.  

DA DUMI-DUMI: EFCC ta dakatar da amfani da Dala, ta umurni Ofisoshin Jakadanci su koma ƙarbar Naira

Image
  DA DUMI-DUMI: EFCC ta dakatar da amfani da Dala, ta umurni Ofisoshin Jakadanci su koma ƙarbar Naira Hukumar EFCC ta umurci ma’aikatan kasashen waje da ke Najeriya da ofisoshin Jakadanci, su daina mu’amala da kudaden waje, su koma yin amfani da Naira wajen gudanar da harkokinsu na hada-hadar kudi,  A Yau ta ruwaito EFCC ta kuma umarci ma’aikatan Najeriya da ke kasashen waje da su karbi Naira a kasuwancinsu na kudi. Hukumar ta ce ta dauki matakin ne domin magance matsalar dala a tattalin arzikin Najeriya da kuma tabarbarewar darajar Naira. LIKE // SHARE & FOLLOW US >

Kamfanoni ne ya kamata su biya harajin tsaron intanet ba mutane ba

Image
  ASALIN HOTO Dama tun tuni akwai dokar tattara harajin tsaro ta intanet a Najeriya, yanzu ne kawai aka fara neman aiwatar da ita, wadannan sune kalaman masanin tattalin arziki Aliyu Da'u Aliyu. Ya bayyana hakan ne a cikin shirin Ra'ayi Riga na BBC Hausa da ake gabatarwa a kowacce Juma'ar ƙarshen mako. Shirin wanda ya samun bakuncin Sanata Shehu Umar Buba wanda ya gabatar da kudurin a gaban majalisar dattijan Najeriya da Honarabil Ali Madakin Gini dan Majalisar wakilan Najeriya da Malam Kabiru Adamu shugaban kamfanin Beacon Consulting kuma masani kan harkokin tsaro da Malam Adam Hassan shugaban kungiyar 'yan tireda na arewacin Najeriya. Yayin tattaunawar da aka yi Aliyu Da'u Aliyu ya ce a mahangarsu ta tattalin arziki babu bukatar ƙara ƙaƙabawa dan Najeriya ƙarin haraji a yanzu, musamman idan aka yi la'akari da halin da ake ciki a ƙasar. Shi kuwa Honarabil Ali Madakingini cewa ya yi, dokar ba ta shafi daidaikun mutane ba. "Ta taƙaita ne kan kamfanonin sadar...

Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina

Image
 ‘Yan sanda sun dakile yunkurin garkuwa da mutane a jihar Katsina Rundunar 'yan sandan jihar Katsina sun yi nasarar dakile yunkurin yin garkuwa da mutane a karamar hukumar Faskari da Malumfashi a jihar, a ranakun 8 da 9 ga watan Mayun 2024. Kakakin rundunar 'yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce ‘yan bindigar sun kai harin farko ne a ranar 8 ga watan Mayu, 2024, bayan sun tare hanyar Funtua zuwa Gusau, a kauyen Unguwar Boka, a karamar hukumar Faskari. A cewarsa, ‘yan ta’ad-dan sun far wa fasinjojin da ke tafiya a cikin wata kirar motar Golf III, inda suka ci da halbe-halbe. Sai dai Sadiq ya bayyana cewa shirin nasu ya ci tura sakamakon wani dauki da jami’an sintiri suka kai. Daily news hausa

WATA SABUWA: Tallafin man fetur da Tinubu ya dawo da shi zai kwashe kusan rabin kudin man fetur da Najeriya za ta sayar – inji IMF

Image
 WATA SABUWA: Tallafin man fetur da Tinubu ya dawo da shi zai kwashe kusan rabin kudin man fetur da Najeriya za ta sayar – inji IMF Asusun bayar da lamuni na duniya, IMF ya yi gargaɗin cewa maido da tallafin man fetur da Najeriya ta yi zai laƙume kusan rabin kudaden shigarta na man fetur a bana, wanda hakan zai hana Gwamnati samun damar aiwatar da ayyukan da ta tsara za ta yi a bana, A cewar IMF tallafin zai janyo wa Najeriya hasarar kudin danyen mai na kusan fiye da dala tiriliyan 8.43 (dala biliyan 5.9) daga cikin kudin da ƙasar ta yi hasashen za ta samu na naira tiriliyan 17.7 na kudin man fetur, in ji IMF a wani rahoto da ta fitar... Daga shafin, A Yau

Chelsea za ta yi nazari,kan makomar Pochettino, Flick zai koma Bayern Munich

Image
  GETTY IMAGES Bayanan hoto, Mauricio Pochettino Chelsea  za ta yi nazarin karshen kakar wasa ta bana bayan wasan karshe na gasar Premier da za ta yi da  Bournemouth , inda za ta yanke shawara kan makomar kocinta Mauricio Pochettino.  (Telegraph) Arsenal  na zawarcin tsohon mai tsaron ragar kungiyar da Poland Wojciech Szczesny, mai shekara 34, da golan Brighton Jason Steele dan Birtaniya da kuma na Ajax Diant Ramaj dan kasar Jamus yayin da su ke neman wanda zai maye gurbin Aaron Ramsdale, mai shekara 25 wanda zai bar Gunners.  (Standard) Har illa yau  Arsenal  na kuma duba yiwuwar daukar golan  Everton  da Ingila Jordan Pickford, mai shekara 30 a wannan bazara.  (Teamtalk) Gunners  na kuma neman dan wasan baya da tsakiya da kuma mai kai hari a kokarin da suke yi domin fadada 'yan wasan kungiyar karkashin jagorancin Mikel Arteta.  (Standard) Graham Potter ya ki amincewa da damar da aka bashi na zama kociyan Ajax, bayan da y...

#innalillahi... Abun yanamin ciwo araina inajin ba dadi. Idan na kalli rayuwata

Image
 #innalillahi... Abun yanamin ciwo araina inajin ba dadi. Idan na kalli rayuwata  Duniya tayi zafi rayuwa Tana neman yin juyin juya Hali..  Ilimi yazama tarihi a unguwanin mu..  Shin menene matsalar NE  A iya fahimtata masu kudin mu Da shuwagabanin mu sune basa kaunar ganiin muncigaba a Harkar ilimi  Sceince sunyi gsky dasuke cewa marabar Dan adam Da dabba shine tunani,hankali, dakuma kwakwalwa Da aikinta..  Ayau anwayi gari ana amfanin Da jahilicin mu wajen maidamu dabbobin kwantarwa ayanka  Ina ganin hakkin mutunne matukar yanada dabba yaciyar Da ita halak Mufa mutanene babu Wanda zai ciyar damu sai Allah.. Toh meyasa Ta karfi dayaji saikun maidamu dabbobi ta hanyar nesantamu Da ilimi   Rayuwar karatun talaka Da dayanxu  Before jamb 2500 but yanzu 5k  Before neco 25k yanzu Kuma 35k Before WA. Ec 30k yanxu 40k  Ana siyasantar mana Da ilimi haba  Yabaxamu jii ba dadiba  Wlh karkuyi tunanin muka Bari suka rabamu D...

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya biya wa daukacin maniyyata aikin bana daga jihar kudin hadaya.

Image
 Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ya biya wa daukacin maniyyata aikin bana daga jihar kudin hadaya. Kudin hadayar kowane Alhaji dai sun kama Riyale 720 kwatankwacin Naira 280,000

Sabon filin jirgin saman Dubai da za a kashe Dala bilyan 35 wajen gina shi

Image
  Sabon filin jirgin saman Dubai da za a kashe Dala bilyan 35 wajen gina shi, da za a kammala aikin rukunin farko a shekaru 10. DW Hausa

Babban Zauren MDD ya nemi Kwamitin Sulhu ya amince da ƙasar Falasɗinu

Image
  Copyright: Reuters BABAN zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi ƙira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar da ya tabbatar da 'yancin Falasɗinawa ta hanyar amincewa da kasar a matsayin mamba a majalisar. Falasɗinu dai na da matsayin ƙasa 'yar sa ido tun shekarar 2012, wani abu da ke nuna rashin cikakken 'yancinta na kasancewarta ƙasa mai 'yancin a zauren. Kwamitin Tsaro na Majalisar ta Dinkin Duniya ne kawai yake da damar tabbatar da hakan. Amurka za ta hau kujerar naƙi dangane da zaman Falasɗinu samun matsayin zaman cikakkiyar mamba a kwmaitin. To sai dai zaɓen na ranar Juma'a ya nuna irin goyon bayan da ake nuna wa ƙasar Falasɗinawa. Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasashen Turai ke ƙoƙarin amincewa da ƙasar Falaɗinawa.

Dalilin mu na maka gwamnonin Najeriya a kotu- SERAP

Image
  ASALIN HOTON, GOV UBA SANI/FACEBOOK Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci da rashawa a Najeriya, ta yi ƙarin haske akan dalilan kai ƙarar gwamnonin ƙasar 36 da kuma ministan birnin tarayyar Abuja gaban kotu. Kungiyar ta ce ta shigar da wannan kara ne saboda rashin bayar da bayanai kan yadda gwamnonin jihohin Najeriya 36 da ministan Abuja, suka kashe kuɗaɗen da suka ciyo na bashin naira tiriliyan kusan shida, da kuma sama da dala billiyan 4 da rabi, ba tare da bahasi ba. SERAP ta buƙaci kotun da ta gayyaci hukumar EFCC da ICPC domin ƙaddamar da bincike kan yadda aka kashe basusukan da gwamnonin suka karɓo. Kungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta ce ta shigar da karar ne a ranar juma'ar makon da ya gabata a babbar kotun tarayya da ke Abuja. SERAP din ta ce, ta shigar da karar ne bayan gazawar gwamnonin wajen yi wa al'ummar su bayanin yadda suka kashe basusukan da suka karɓo da wajen da aka aiwatar da auikin da aka karbo bashin dominsu. Kolawole Olu...

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga a Neja da Borno

Image
  ASALIN HOTO Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakarunta sun samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama a jihohin Borno da Neja. Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin saman ƙasar, Edward Gabkwet ya ce cikin jerin wasu hare-hare ta sama da dakarun rundonin Hadin Kai da Whirl Punch suka ƙaddamar a jihohin biyu ya samu narasar lalata wasu shirye-shiryen 'yan bindigar. Edward Gabkwet ya ce a ranar 3 ga watan Mayu dakarun ƙasar sun kai hari a garin Chinene da ke yankin tsaunin Mandara da ke kusa da jihar Borno. Ya ce dakarun sojin ƙasar sun ga 'yan bindigar na wani taro da ake kyautata zaton tattaunawa suke yi a lokacin da jirgin sojin ya kai musu hari tare da kashe su. “Haka kuma a garin sojojinmu sun hangi wasu motocin yaƙi bakwai da ake zaton na 'yan bindigar ne a ƙarƙashin wata bishiya, nan take su ma aka kai musu hari tare da lalata su'', in ji sanarwar. Sanarwar ta ƙara da cewa “bayanan da muka samu bayan hare-haren sun nuna cewa an samu nasara...

HOTONAN Yadda Kabilar Dakarkari ke cigaba da gudanar da wasannin al'adun Gargajiya Zuru Uhola.

Image
HOTONAN Yadda Kabilar Dakarkari ke cigaba da gudanar da wasannin al'adun Gargajiya Zuru Uhola. Bikin raya al'adun Gargajiya na kabilar Dakarkari dake masarautar Zuru a jihar kebbi biki ne da ake gudanarwa domin nuna godiya ga Allah. Dubban al'umma ne ciki da wajen jihar suka halarci taron ciki hadda dan majalisar tarayyar Najeriya mai wakiltar masarautar Zuru Hon Kabir Ibrahim Tukura. Hoto📷 Abbakar Aleeyu Anache