Posts

Dakarun Najeriya sun kuɓutar da mutane daga hannun masu garkuwa a Taraba b

Image
  Kanawa post news  Rundunar sojin Najeriya tare da haɗin gwiwar wasu jami'an tsaro, sun lalata wata maɓoyar masu garkuwa da mutane tare da kuɓutar da mutum huɗu da aka yi garkuwa da su a yankin ƙaramar hukumar Yorro na jihar Taraba. Cikin wata sanarwa da mai riƙon muƙamin daraktan yaɗa labaran rundunar sojin Najeriya ta 6 da ke jihar, Laftanar Oni Olubodunde ya sanya wa hannu, ya ce sojojin sun ƙaddamar da yaƙi da 'yan bindigar ne tun da suka yawaita kai hare-hare a yankin ƙaramar hukumar. Ya ƙara da cewa dakarunsu sun yi gumurzu da masu garkuwar a tsaunukan Gampu da na Ban Yorro, bayan musayar wuta tsakanin ɓangarorin ne, sai 'yan bindigar suka arce inda suka bar mutum huɗu da suka yi garkuwa da su. Sanarwar ta ƙara da cewa sojojin za su ci gaba da aiki a yankin har sai sun tabbatar da kuɓutar da sauran mutanen da ke hannun masu garkuwar.

Tinubu ya aike da ta'aziyyarsa kan rasuwar shugaban Namibiya

Image
Bola Ahmed Tinubu/XCopyright: Bola Ahmed Tinubu/X Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aike da saƙon ta'aziyyarsa ga al'ummar Namibiya bisa rasuwar shugaban ƙasar Hage Geingob. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Ajuri Ngelale ya fitar, shugaba Tinubu ya ce ya kaɗu da jin labarin rasuwar mista Geingob, wanda ya bayyana da ɗan kishin gwagwarmayar tabbatar da dimokraɗiyya. Shugaban na Najeriya ya kuma bayyana marigayin da jagoran tabbatar da jagoranci nagari, da bunƙasa tattalin arziki da ci gaba al'ummar Afirka. Shugaba Tinubu ya ce marigayin ya rasu ne a daidai lokacin da nahiyar Afirka ke buƙatar jajirtattun shugabanni irinsa, waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu wajen bunƙasa nahiyar ta ko wanne fannin ci gaba. Daga ƙarshe shugaba Tinubu ya ce a madadin gwamnatinsa da al'ummar Najeriya suna miƙa saƙon ta'aziyyarsu ga ɗaukacin al'ummar Nambiya bisa wannan babban rashi da suka yi. Hage Geingob: Shugaban Namibia ya rasu yana dan shekara 82 Article...

Mayakan ISWAP sun kashe 'yan sanda hudu a harin da suka kai a Borno

Image
G NPFCopyright: NPF Aƙalla 'yan sanda hudu ne suka rasa ransu sannan aka kwashe dimbin harsasai masu yawa a wani hari da ake zargin mayaƙan ISWAP ne suka kai ofishin 'yan sanda a Ƙaramar Hukumar Nganzai da ke Borno. Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mayakan ISWAP sun kutsa kai ne cikin ofishin 'yan sandan tare da buɗe wuta kan jami'an da suke aiki. A cewar majiyar tsaro, mahairan sun ƙona wani ɓangare na ofishin 'yan sandan lokacin da abin ya faru a ranar Juma'a. "An samu ruɗani a garinmu a daren jiya. MMayaƙan ISWAP sun kai wa ofishin 'yan sanda hari a Gajiram. Kuma gaskiya sun fi ƙarfin jami'an da suke kan aiki." "Mun samu gawar 'yan sanda hudu a yashe a inda abin ya faru da safiyar yau, har yanzu ba a ga wasu 'yan sandan da suka tsere ba," in ji wani jami'in 'yan sa-kai. Rahotanni sun ce maharan sun bar wurin tun gabanin sojoji su isa.  

INEC ta dakatar da zaɓen cike giɓi a wasu rumfunan Kano da Enugu da Akwa Ibom

Image
Kanawa post news  Hukumar zaɓen Najeriya ta sanar da dakatar da zaɓukan cike giɓi da ake gudanarwar a jihohin Kano da Enugu da Akwa Ibom. Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta ce ta ɗauki matakin ne sakamakon matsalolin da aka samu na satar da kayan zaɓe da yin garkuwa da wasu jami'an zaɓe a jihohin. Sanarwar ta ce wuraren da lamarin ya shafa sun haɗar da rumfuna biyu a mazaɓar tarayya ta Ikono/Ini a jihar Akwa Ibom, inda INEC din ta ce aka samu wasu ɓata-gari suka lalata kayan zaɓen. A jihar Enugu kuwa da ke kudu maso gabashin ƙasar, hukumar zaɓen ta ce an fitar da takardun sakamako tun kafin fara zaɓe a rumfuna takwas. A ƙananan hukumomin Kunchi da Tsanyawa kuma, INEc din ta ce an samu hatsaniya a rumfunan zaɓe 10, inda 'yan daba suka lalata kayan zaɓe tare da hana gudanar da zaɓen. Hukumar zaɓen ta ce ta yi aiki da sashen dokar zaɓen na 24 wajen dakatar da zaɓen. Hukumar ta kuma yi kira ga jami'an tsaro da su gudanar da bincike kan lamurran, inda hukumar ta ce tana ...

Syria ta zargi Amurka da iza wutar rikici a Gabas ta Tsakiya

Image
a Kanawa post news  Ma'aikatar Harkokin Wajen Syria ta yi Allah-wadai da harin da Amurka ta kai da daren jiya a Iraƙi da Syria. Cikin wata sanarwa da aka wallafa a kamfanin dillancin labarai na ƙasar SANA, ta ce harin da Amurka ta kai ya sake tabbatar da abin da ake zargi na cewa, dakarunta na barazana ga zaman lafiyar duniya, kuma ita take iza wutar rikicin da yake faruwa a yakin Gabas ta Tsakiya." Gwamnatin Syria dai na adawa da kasancewar Amurka a cikinta kuma tana ɗaukar hakan a matsayin mamaya. A bara ne Syria ta koma cikin ƙungiyar ƙasahen Larabawa, bayan sama da shekara 10 da aka koreta daga ƙungiyar saboda muguntar da ta nuna kan masu rajin dimokraɗiyya lokacin da suke zanga-zanga, wani abu da ya tayar da rikicin basasa. Amurka da Burtaniya da wasu sauran ƙasashen yamma sun soki komawar Syria cikin ƙungiyar, kuma a bayan nan sun jaddada cewa ba za su dawo hulɗar diflomasiyya ba da shugaban Syrian Shugaba Bashar al-Assad. Article share tools

Muna da ƙwarin gwiwar doke Angola - Ekong

Image
  ASALIN HOTON, GETTY IMAGES Bayanan hoto, Najeriya za ta buga wasanta na 11 a matakin daf da na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka - babu wata ƙasa da ta kai ta buga wasanni a wannan mataki na gasar. Bayani kan maƙala Marubuci, Emmanuel Akindubuwa and Isaiah Akinremi Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa, Lagos Sa'o'i 5 da suka wuce Kyaftin din tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya William-Troost Ekong ya ce Super Eagles na da ƙwarin guiwar yin nasara a kan Angola a gasar cin kofin Afrika ta 2023 lokacin da ƙungiyoyin za su fafata a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a Ivory Coast. Wannan shi ne karon farko da za a yi gwagwarmaya a gasar Afcon tsakanin Najeriya da Angola, amma haɗuwar da aka yi a baya tsakanin ƙasashen na nuni da cewa wasan da za a buga a filin wasa na Felix Houphouet-Boigny da ke Abidjan. Najeriya wadda ta lashe kofin sau uku a yanzu ita ce ta ɗaya a matsayi mafi girma da ta rage a gasar bayan an yi waje da Senegal mai riƙe da kofin, da...

An samu mummunar fashewa a Kenya KenyaASALIN HOTON, REUTERS

Image
Sa'o'i 2 da suka wuce Akalla mutum biyu aka tabbatar da sun mutu yayin da sama da 300 suka jikkata sakamakon wata mummunar fashewa a wata cibiyar sayar da gas din girki a Nairobi na Kenya. Cibiyar gas din na rukunin gidajen al’umma. Hotunan Bidiyon a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wuta da hayaki suka turmuke saman rukunin benaye yayin da mutane suka shiga firgici da ruɗani domin neman tsira. Mazauna yankin Embakasi da ke kudu maso gabashin Nairobi sun ce sun ji kamar girgiza kafin ganin haske a sama a tsakar dare. Wani mazauni yankin wanda ya ce a gabansa fashewar ta auku Boniface Sifuna ya ce ta ƙyar ya tsira duk da ya samu ƙuna a jikinsa. An bayyana cewa wutar ta bazu inda ta ci gidaje da dama. Jami’an kashe gobara da jami’an agajin gaggawa sun isa wurin Kakakin gwamnatin Kenya ya ce fashewar ta faru ne a wata cibiyar da ake sayar da gas din girki. Kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce ta kai wasu mutane 29 da suka samu munanan raunuka zuwa babban asibitin kasar da ...
Image
 Sadio Mane: “Ina mai baki haƙuri Mata ta, Bazan iya kawo miki kofin da kika buƙata a matsayin kyautar Auren mu ba, Nayi iya bakin ƙoƙarina amma hakan bai wadatar na samu kofin ba ina mai baki haƙuri.”

labarai suna tambayar ‘Wai me yasa har yanzu ba a ga Ahmed Musa a cikin fili ba’. Kamar

Image
 labarai suna tambayar ‘Wai me yasa har yanzu ba a ga Ahmed Musa a cikin fili ba’. Kamar yadda kuka sani wannan ba sabon abu bane. “Komai nufi ne na Allah, Idan Allah yaso Ni zan shiga na sauya wasa. Ko kuma Ni zan kawo sakamakon abun da ake nema shikenan, Kawai ni fata na a cigaba da yimin da kuma ƙungiyar mu Addu'a duk mai haƙuri yana tare da samu. “Nasara muke buƙata duk wanda yake cikin fili indai yanayin abun da Yakamata to mu bashi goyon baya. Duk randa Allah yayi na shigo kuma na zama silar naasarar mu hakan shine rabo na, Kuma babu wanda yake tsallake wa rabon sa.” - In ji - Ahmed Musa Kyaftin ɗin Super Eagles a zantawar sa da RFI Hausa.  

EFCC na bincike kan yarjejeniyar Nigeria Air - Keyamo

Image
Copyright: Nigerian Govt Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya Festur Keyamo ya ce hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC na gudanar da bincike kan yarjejeniyar kamfanin jiragen sama na ƙasar wato 'Nagerian Air' mai cike da ce-ce-ku-ce da gwamnatin tarayya ta ƙulla ƙarƙashin tsohon ministan kula da sufurin jiragen sama na ƙasar Hadi Sirika Yayin da yake zantawa da gidan talbijin na Channels ranar Laraba, mista Keyamo ya ce “EFCC na bincike kan yarjejeniyar. ''Ana gudanar da bincike kan lamarin, kuma muna jiran rahoton binciken''. Mista Keyamo wanda suka yi aiki tare da Siriki a matsayin ministocin gwamnatin Buhari, ya ce babu wani kamfanin jirage da ke aiki a matsayin kamfanin jirage na ƙasa, amma ya ce za a samar da nagartaccen kamfanin jirage na ƙasa. A watan Agustan bara ne Mista Keyamo ya ƙaryata yarjejeniyar da Sirika ya ƙulla tare da dakatar da duk wani shiri da ke cikin yarjejeniyar. Batun yarjejeniyar kamfanin 'Nigerian Air' da...