An samu mummunar fashewa a Kenya KenyaASALIN HOTON, REUTERS
Sa'o'i 2 da suka wuce
Akalla mutum biyu aka tabbatar da sun mutu yayin da sama da 300 suka jikkata sakamakon wata mummunar fashewa a wata cibiyar sayar da gas din girki a Nairobi na Kenya.
Cibiyar gas din na rukunin gidajen al’umma.
Hotunan Bidiyon a kafafen sada zumunta sun nuna yadda wuta da hayaki suka turmuke saman rukunin benaye yayin da mutane suka shiga firgici da ruɗani domin neman tsira.
Mazauna yankin Embakasi da ke kudu maso gabashin Nairobi sun ce sun ji kamar girgiza kafin ganin haske a sama a tsakar dare.
Wani mazauni yankin wanda ya ce a gabansa fashewar ta auku Boniface Sifuna ya ce ta ƙyar ya tsira duk da ya samu ƙuna a jikinsa.
An bayyana cewa wutar ta bazu inda ta ci gidaje da dama. Jami’an kashe gobara da jami’an agajin gaggawa sun isa wurin
Kakakin gwamnatin Kenya ya ce fashewar ta faru ne a wata cibiyar da ake sayar da gas din girki.
Kungiyar agaji ta Red Cross ta Kenya ta ce ta kai wasu mutane 29 da suka samu munanan raunuka zuwa babban asibitin kasar da ke Nairobi.
‘Yan kasar da dama na tambayar dalilin da ya sa aka bar irin wannan cibiyar gas mai hatsari kusa da gidajen al’umma.
Comments