Muna da ƙwarin gwiwar doke Angola - Ekong
- Emmanuel Akindubuwa and Isaiah Akinremi
- BBC Sport Africa, Lagos
Kyaftin din tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya William-Troost Ekong ya ce Super Eagles na da ƙwarin guiwar yin nasara a kan Angola a gasar cin kofin Afrika ta 2023 lokacin da ƙungiyoyin za su fafata a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a Ivory Coast.
Wannan shi ne karon farko da za a yi gwagwarmaya a gasar Afcon tsakanin Najeriya da Angola, amma haɗuwar da aka yi a baya tsakanin ƙasashen na nuni da cewa wasan da za a buga a filin wasa na Felix Houphouet-Boigny da ke Abidjan.
Najeriya wadda ta lashe kofin sau uku a yanzu ita ce ta ɗaya a matsayi mafi girma da ta rage a gasar bayan an yi waje da Senegal mai riƙe da kofin, da Morocco da ta kai wasan dab da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya da kuma Masar wadda ta lashe gasar sau bakwai.
"Wannan gasar ta koya mana abubuwa da yawa. Babu wata babbar ƙungiya ko ƙarama kuma," in ji Troost-Ekong mai tsaron bayan Super Eagles.
"Muna da ƙwazo sosai saboda mun gan yadda Angola take wasa, kuma tana da ‘yan wasa masu kyau."
Yayin da Super Eagles ke shirn karawa da Palancas Negras, ramuwar gayya na iya zama ɗaya daga cikin abubuwan da tawagar Najeriya za ta yi tunani domin shafe baƙin cikin da ta samu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a shekara ta 2006 a hannun Angola.
Angola ta hana tawagar Najeriya wanda ke cike da taurarin 'yan wasan da suka haɗa da Jay-Jay Okocha da Joseph Yobo da Nwankwo Kanu da Yakubu damar zuwa gasar 2006 a Jamus, inda 'yan wasan Angolan suka tsallake rijiya da baya bayan da kungiyoyin biyu suka kare da maki 21 a rukuni na 4.
'Yan wasan Angola sun doke Najeriya a Luanda da ƙwallon da suka ci a minti na 86 wanda Akwa ya zura musu, sannan suka yi kunnen doki da Super Eagles da ci 1-1 a gidan Najeriya.
Duka ɓangarorin biyu sun samu nasarar fafatawarsu biyu na ƙarshe yayin da Palancas Negras ta yi nasarar samun gurbinta na farko a gasar cin kofin duniya.
Troost-Ekong ya yi imanin cewa 'yan wasan Super Eagles na yanzu za su koyi darasi daga wannan rashin nasaran kuma ba za su raina 'yan Angolan da suka yi fice a gasar ba.
"Zai kasance wasa mai wahala. Za mu tunkare shi kamar yadda muka tunkari kowane wasa wanda shi ne mu je neman nasara," in ji ɗan wasan mai shekara 30.
"Ina ganin mun warware yayin da gasar ke ci gaba, kuma za mu nemi yin hakan a yanzu."
Daga gaba ake fara tsaron baya- Lookman
Najeriya, wadda ke matsayi na 42 a duniya, a yanzu ta kasance wadda ake ganin za ta iya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023, bayan fitar da manyan ƙasashen nahiyar da dama kafin wasan daf da na kusa da ƙarshe.
Tuni dai Morocco mai matsayi na 13 da Senegal mai riƙe da kofin gasar wanda ke matsayi na 20 da Tunisia ta 28 da Aljeriya ta 30 da Masar ta 33, duk sun riga sun yi waje daga gasar.
Ita kuwa Angola, ita ce kurar baya a gasar, tana matsayi na 117 a duniya, kuma za ta zo da niyyar samun wani sakamako mai ban mamaki kamar yadda aka gani a gasar bana.
Bisa ƙididdigar da kamfanin Opta ta yi, Najeriya ce ke kan gaba wajen damar lashe gasar - da kusan kashi 28.8% - kuma tana da damar doke Angola da kashi 55.5 cikin ɗari cikin mintuna 90.
Ademola Lookman - wanda ya zura ƙwallaye biyun da Najeriya ta ci Kamaru a wasan zagaye na biyu - ya ce "muna a matakin daf da na kusa da ƙarshe, ba sa’a ce kaɗai ta kawo mu nan ba, ƙungiya ce mai kyau, don haka muna buƙatar mu shirya musu da kyau."
"Za su fito domin tabbatar da cewa ba mu fi ƙarfinsu ba, tunanin yanzu shi ne mu tsaya kan yadda wasanmu yake kuma mu ɗauke su da muhimmanci," in ji mai tsaron baya Kenneth Omeruo, wanda yana cikin tawagar Super Eagles da ta lashe Afcon a 2013.
Bayan buɗe gasar da kunnen doki 1-1 da Algeria, a yanzu Angola ta ƙara samun nasara a wasanni uku a gasar inda ta doke Mauritania da Burkina Faso da kuma Namibia.
Ɗan wasan gaba Gelson Dala, wanda ya taka rawar gani da ƙwallaye huɗu a gasar - ciki har da biyu a wasan da suka doke Namibia a zagaye na biyu- shi ne zai kasance babban barazanar da Angola za ta yi wa Super Eagles, wanda ba a zura mata ƙwallo ko ɗaya ba a wasanni uku.
"Tsaron bayan mu na farawa ne daga gaba," in ji Lookman.
"Yana da mahimmanci a gare mu. Ina tsammanin mun yi tsayin daka kan tsaron baya kuma ya taimaka mana a harin da muke kai wa daga gaba."Muna da ƙwarin gwiwar doke Angola - Ekong
William Troost-Ekong and Frank Onyeka in Super Eagles coloursASALIN HOTON, GETTY IMAGES
Bayanan hoto,
Najeriya za ta buga wasanta na 11 a matakin daf da na kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin nahiyar Afirka - babu wata ƙasa da ta kai ta buga wasanni a wannan mataki na gasar.
Bayani kan maƙala
Marubuci, Emmanuel Akindubuwa and Isaiah Akinremi
Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Sport Africa, Lagos
Sa'o'i 5 da suka wuce
Kyaftin din tawagar ƙwallon ƙafar Najeriya William-Troost Ekong ya ce Super Eagles na da ƙwarin guiwar yin nasara a kan Angola a gasar cin kofin Afrika ta 2023 lokacin da ƙungiyoyin za su fafata a wasan daf da na kusa da na ƙarshe a Ivory Coast.
Wannan shi ne karon farko da za a yi gwagwarmaya a gasar Afcon tsakanin Najeriya da Angola, amma haɗuwar da aka yi a baya tsakanin ƙasashen na nuni da cewa wasan da za a buga a filin wasa na Felix Houphouet-Boigny da ke Abidjan.
Najeriya wadda ta lashe kofin sau uku a yanzu ita ce ta ɗaya a matsayi mafi girma da ta rage a gasar bayan an yi waje da Senegal mai riƙe da kofin, da Morocco da ta kai wasan dab da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya da kuma Masar wadda ta lashe gasar sau bakwai.
"Wannan gasar ta koya mana abubuwa da yawa. Babu wata babbar ƙungiya ko ƙarama kuma," in ji Troost-Ekong mai tsaron bayan Super Eagles.
"Muna da ƙwazo sosai saboda mun gan yadda Angola take wasa, kuma tana da ‘yan wasa masu kyau."
Yayin da Super Eagles ke shirn karawa da Palancas Negras, ramuwar gayya na iya zama ɗaya daga cikin abubuwan da tawagar Najeriya za ta yi tunani domin shafe baƙin cikin da ta samu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya a shekara ta 2006 a hannun Angola.
Angola ta hana tawagar Najeriya wanda ke cike da taurarin 'yan wasan da suka haɗa da Jay-Jay Okocha da Joseph Yobo da Nwankwo Kanu da Yakubu damar zuwa gasar 2006 a Jamus, inda 'yan wasan Angolan suka tsallake rijiya da baya bayan da kungiyoyin biyu suka kare da maki 21 a rukuni na 4.
'Yan wasan Angola sun doke Najeriya a Luanda da ƙwallon da suka ci a minti na 86 wanda Akwa ya zura musu, sannan suka yi kunnen doki da Super Eagles da ci 1-1 a gidan Najeriya.
Duka ɓangarorin biyu sun samu nasarar fafatawarsu biyu na ƙarshe yayin da Palancas Negras ta yi nasarar samun gurbinta na farko a gasar cin kofin duniya.
Troost-Ekong ya yi imanin cewa 'yan wasan Super Eagles na yanzu za su koyi darasi daga wannan rashin nasaran kuma ba za su raina 'yan Angolan da suka yi fice a gasar ba.
"Zai kasance wasa mai wahala. Za mu tunkare shi kamar yadda muka tunkari kowane wasa wanda shi ne mu je neman nasara," in ji ɗan wasan mai shekara 30.
"Ina ganin mun warware yayin da gasar ke ci gaba, kuma za mu nemi yin hakan a yanzu."
Daga gaba ake fara tsaron baya- Lookman
Nigerian players celebrating after a goalASALIN HOTON, GETTY IMAGES
Bayanan hoto,
Najeriya ta buga wasanni uku a jere a gasar 2023 ba tare da an zura mata ƙawallo ko ɗaya a raga ba
Najeriya, wadda ke matsayi na 42 a duniya, a yanzu ta kasance wadda ake ganin za ta iya lashe gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2023, bayan fitar da manyan ƙasashen nahiyar da dama kafin wasan daf da na kusa da ƙarshe.
Tuni dai Morocco mai matsayi na 13 da Senegal mai riƙe da kofin gasar wanda ke matsayi na 20 da Tunisia ta 28 da Aljeriya ta 30 da Masar ta 33, duk sun riga sun yi waje daga gasar.
Ita kuwa Angola, ita ce kurar baya a gasar, tana matsayi na 117 a duniya, kuma za ta zo da niyyar samun wani sakamako mai ban mamaki kamar yadda aka gani a gasar bana.
Bisa ƙididdigar da kamfanin Opta ta yi, Najeriya ce ke kan gaba wajen damar lashe gasar - da kusan kashi 28.8% - kuma tana da damar doke Angola da kashi 55.5 cikin ɗari cikin mintuna 90.
Ademola Lookman - wanda ya zura ƙwallaye biyun da Najeriya ta ci Kamaru a wasan zagaye na biyu - ya ce "muna a matakin daf da na kusa da ƙarshe, ba sa’a ce kaɗai ta kawo mu nan ba, ƙungiya ce mai kyau, don haka muna buƙatar mu shirya musu da kyau."
"Za su fito domin tabbatar da cewa ba mu fi ƙarfinsu ba, tunanin yanzu shi ne mu tsaya kan yadda wasanmu yake kuma mu ɗauke su da muhimmanci," in ji mai tsaron baya Kenneth Omeruo, wanda yana cikin tawagar Super Eagles da ta lashe Afcon a 2013.
Bayan buɗe gasar da kunnen doki 1-1 da Algeria, a yanzu Angola ta ƙara samun nasara a wasanni uku a gasar inda ta doke Mauritania da Burkina Faso da kuma Namibia.
Ɗan wasan gaba Gelson Dala, wanda ya taka rawar gani da ƙwallaye huɗu a gasar - ciki har da biyu a wasan da suka doke Namibia a zagaye na biyu- shi ne zai kasance babban barazanar da Angola za ta yi wa Super Eagles, wanda ba a zura mata ƙwallo ko ɗaya ba a wasanni uku.
"Tsaron bayan mu na farawa ne daga gaba," in ji Lookman.
"Yana da mahimmanci a gare mu. Ina tsammanin mun yi tsayin daka kan tsaron baya kuma ya taimaka mana a harin da muke kai wa daga gaba."
Comments