Posts

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Image
Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai buɗe  taron yaƙi da ta'addanci na Afirka da za a gudanar a Abuja fadar gwamnatin ƙasar. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban na Najeriya, Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce taron - wanda Najeriya da haɗin gwiwar ofishin yaƙi da ta'addanci na Majalisar Dinkin Duniya suka shirya - za a fara shi ranar Litinin 22 ga watan Afrilu. Manufar taron ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa don yaƙi da ta'addanci a ƙasashen Afirka tare da sake fasalin yadda duniya ke kallon ta'addanci a Afirka, da kuma lalubo sabbin hanyoyin magance matsalar a faɗin nahiyar. Ana sa ran shugabannin gwamnatoci da manyan jami'an gwamnatocin ƙasashen Afirka, da wakilan ƙungiyoyin duniya da cibiyoyi, da jami'an diplomasiyya da ƙungiyoyin fararen hula za su halarci taron. Sanarwar ta ƙara da cewa ana sa ran mataimakiyar babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Amina Mohammed za ta halarci taron. ''Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro Malla...

An rufe Jami'ar Jihar Plateau bayan mutuwar wani ɗalibi

Image
Copyright: PLATEAU STATE UNIVERSITY, BOKKOS/ FACEBOOK Jami’ar Jihar Filato, da ke Bokkos, ta dakatar da dukkan harkokin koyarwa a makarantar har na tsawon kwanaki goma, bayan wani hari da aka kai da ya hallaka wani ɗalibi. Ɗalibin wanda ke matakin aji biyu (200 level) a fannin kimiyyar na'ura mai kwakwalwa ya gamu da ajalinsa ne ranar Juma'a a harin da wasu suka kai harabra jami'ar. Wani malamin jami'ar, Yakubu Ayuba, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, ya ce, “Bayan wani abin bakin ciki da ya faru a jami’ar Jihar Filato, Bokkos, da kewaye a ranar Juma’a, 19 ga Afrilu, 2024; kuma bisa la’akari da illolin da wannan al'amari zai yi wa ɗalibai da ma’aikatan jami’ar, hukumar gudnarwa ta ɗauki matakin rufe jami’ar na tsawon kwanaki 10 daga ranar 19 ga Afrilu, 2024. Yakubu ya ce an yi haka ne don ba da dama na ganin yanayin tsaro ya inganta a jama'ar. "Don haka, an dakatar da jarabawar zangon karatu na farko da ake ci gaba da yi, inda za a koma rubuta ta r...

Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo

Image
Bayanan hoto, Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello Ministan shari'ar Najeriya ya bayyana takaici kan yadda ya ce wasu 'yan siyasa ke kange kansu daga kamu bisa wasu laifuka da ake zargin sun aikata. Chief Lateef Olasunkanmi Fagbemi (SAN) ya bayyana hakan ne biyo bayan kulli-kurciyar da aka yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da jami'an hukumar EFCC inda a 'karshe suka kasa damke shi sakamakon kange shi da ake zargin wani jami'in gwammnati ya yi. Al'amarin ya sanya Minstan shari'a ya gargadi jami'an gwamnati wadanda dokar 'kasa ke karewa su guji kawo cikas a kokarin da ya cancanci yabo da hukumar EFCC ke yi. Mai sharhi, Barrister Audu Bulama Bukarti ya bayyana cewar akwai bukatar wannan gargadi abu ne da ya zama wajibi. '' Ita hukumar EFCC, hukuma ce da dokar Najeriya ta kafa ta kuma ba ta ikon ta binciki wanda ake zargi da laifi kuma wanda ake zargi da laifin komai girmansa a 'kasar''. Barrista Bulama ya kuma kar...

NASIHOHI GUDA HAMSIN (50)

Image
1 ka kula da kanka 2 yazamana kana jin tsoron Allah 3 ka san cewa duk abinda ya sameka daga Allah ne 4 ka zamu mai cika alkawari 5 ka zauna da kowa lafiya 6 ka dinga tunawa da mutuwa 7 ka rage buri 8 ka cire kwadayi 9 banda yin hassada don kaga Allah ya daukaka wani 10 kasan cewa ita fa duniya ba matabbaciya bace 11 ka yawaita istigifari 12 ka yawaita salati ga manzon Rahama 13 banda yin gulma ko munafurci 14 banda cin amana 15 ka zauna da kowa lafiya 16 ka tsarkaka zuciyarka 17 banda nufar mutum da sharri 18 karkayi zalunci 19 karkayi girman kai 20 karkayi wulakanci 21 ka zama mai taimako 22 ka kula da addininka 23 ka zamu mutum mai Alkunya 24 ka zama mutum nagari mai kirki 25 kasan cewa komai mai wucewa ne 26 ka dinga hakuri kar ama shaidar cewa baka da hakuri 27 ka kuma yawaita addu'a 28 kayi biyyah ga iyayenka 29 ka zama mai tausayi 30 ka zama mai imani 31 kana aiki da hankalinka 32 ka guje wa sabon Allah 33 karka ci haram 34 karkayi shaye-shaye 35 ka nisanci zina 36 ka mai da ...

Kotun Kano ta ɗage zaman tuhumar Ganduje

Image
Copyright: Socail Media Wata babbar kotu da ke Kano ta ɗage sauraron tuhumar da gwamnatin jihar ke yi wa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje kan cin hanci da rashawa. Bayanai sun nuna cewa kotun ta ɗauki matakin ne saboda rashin sanar da waɗanda ake ƙara batun shari’ar. Mai Shari’a Usman Na’abba ne ya ba da umarnin ɗage ƙarar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu bayan da lauyan mai gabatar da ƙara Y. A. Adamu ya sanar da kotun cewar dukkan yunƙurin da suka yi na sanar da waɗanda ake ƙara ya ci tura. Sai dai lauyan Ganduje, Barista Musa Lawan ya ce tun da fari rashin sanar da su ƙarar da aka shigar ne ya sa suka ƙaurace wa zaman, amma yanzu suna jiran a sanar da su. Gwamnatin Kano na tuhumar Ganduje  matarsa da ɗansa da kuma wani abokinsa da aikata laifuka takwas, waɗanda suka danganci cin hanci da rashawa. Latsa hoton ƙasa ku saurari ƙarin bayanin da lauyan Ganduje, Musa Lawan ya yi wa Khalifa Shehu Dokaji:

Yadda gwamnatin jihar Katsina ta rarraba wa jami'an tsaro motocin yaƙi

Image
  ASALIN HOTON, KATSINA STATE GOVERMENT Bayani kan maƙala Marubuc Sanya sunan wanda ya Gwamnatin jihar Katsina ta rarraba motocin yaƙi ga jami'an tsaro domin shawo kan matsalar tsaro a ƙananan hukumomin da aka fi fuskantar hare-haren ƴanbindiga. Gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda ne ya ƙaddamar da rabon motocin a ranar Litinin. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Katsina, Dakta Nasiru Mu'azu ya shaida wa BBC cewa sun yi la'akari ne da halin da ake ciki, kuma ita wannan mota mai sulke na taimaka wa wajen yaƙin da suke da ƴan bindiga. Gwamnatin ta jihar Katsina ta rarraba motocin guda 10 ne ga jami'an tsaro na ƴan sanda da sojoji da kuma ƴan sa-kai da gwamnatin ta dauka a kwanakin baya domin taimakawa wajen yaƙi da ƴan bindiga a jihar." ASALIN HOTON, KATSINA STATE GOVERMENT Mun yi maganin masu bai wa ƴan bindiga bayanai-Gwamna Dikko Radda 11 Fabrairu 2024 Gane Mini Hanya tare da Gwamnan Katsina Dikko Radda 21 Oktoba 2023 'Ƴanbindiga ...

Fargaba ta ƙaru a ranar Asabar, yayin da jama'ar Iran suka shiga tsoro don gudun

Image
  Fargaba ta ƙaru a ranar Asabar, yayin da jama'ar Iran suka shiga tsoro don gudun kada Isra'ila da mayar da ƙawayen ta su martani. jama'a sun razana sosai ta yadda ake ta rige rigen siyan kayan abinci da man fetir da kuma sauran abubuwan buƙata. An samu dogayen layin man fetir a gidajen mai da ke birnin Tehran da ma sauran manyan birane, yayin da jama'a suka cika manyan kantuna domin siyan kayan buƙata, Duk da cewa Isra'ila ta yi Iƙirarin cewa ta daƙile kashi 99 cikin dari na makamai masu linzami da Iran ta harba mata, jami'an gwamnatoin Iran suna murna ne a kan abin da suka kira nasarar yin abin da ba a taɓa yi a can baya ba. Babban hafsan sojin Iran, Manjo Janar Mohammad Bagheri, ya bayyana cewa daga cikin wuraren da suka kai harin akwai harda wata barikin sojin sama, inda jirgin saman inda kuma daga can ne jirgin Isra'ila samfarin F35s ya tashi har ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun Iran 7, a birnin Damascu. Ya bayyana yaqinin cewa Iran ta cimma nasarar a...

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano

Image
    Copyright: Other Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan al’amarin da ya biyo bayan zargin fille kan wani karamin yaro ɗan shekara shida da wani almajiri ya yi a kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Madobi. Rahotanni dai sun nuna cewa almajirin mai shekaru 22 ya kashe yaron ne a kusa da wata makarantar firamare kafin ya cire kansa. Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya shaida wa BBC cewa almajirin bayan ya yanke wa yaron kai ya jefa da kan a cikin wani masai. "A jiya ne aka wayi gari da wannan labari da ke cewa wasu masu ruwa da tsaki suka lura da cewa sun ga wani yaro a wannan ƙauye da wuƙa wanda suka ga alamun jini a jikin wuƙar kamar jinin ɗan Adam ne, Hakan ne ya sa suka zarge abin da ya sa 'yan unguwa suka cafke shi, suka tasa shi gaba, sai suka ga gangar jikin mutum inda ya amsa shi ne ya kashe shi. Bayan da ƴan sanda suka je, shi ne ya ja su ya kai su inda ya wurgar da kan, inda suka ga kan yaron." In ji kwamishinan 'ya...

Yau take sallah barka da sallah

Image
Ya ce ƙwarewarsu da rashin bai wa abokan kulɗa kunya wajen shirya abincin fita-kunya kamar tuwon sallah cikin gwaninta sun sa mutane na ƙara neman ƙwararrun masu dafa abinci. Ko ba komai, in ji shi, ba a ko'ina ake samun ɗanɗano da daɗi da iya tsara dafaffen abinci mai rai da lafiya a kwano, da ƙamshin burgewa ba. "A kawo muku har gida, ba tare da kun san wata wahalar da aka yi ba, kawai ci kuka sani" in ji mai gidan abincin. "Sai dai ku ci, ku ji daɗi, shi ma wanda aka ba, ya ci ya ji daɗi. Sai a yi ta tunanin ta yaya aka yi haka?" Mata da yawa kamar Ni'ima Ibrahim, ba lallai su yarda da wannan ra'ayi ba. Suna ganin duk da zamani, amma girki ya fi yarda da hannun mata. Hatta naƙaltar yadda ake shirya tuwon sallah, ba abu ne da ke buƙatar wuta-wuta da riƙon maza ba. Gwanintar mata ta fi tashi a girkin tuwon sallah Mata suna bai wa girkin tuwon sallah wata kulawa ta musamman, cewar Dr Hadiza Koko. "Mace du wadda take, in aka ce tuwon sallah za ta yi....