Kotun Kano ta ɗage zaman tuhumar Ganduje
Wata babbar kotu da ke Kano ta ɗage sauraron tuhumar da gwamnatin jihar ke yi wa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje kan cin hanci da rashawa.
Bayanai sun nuna cewa kotun ta ɗauki matakin ne saboda rashin sanar da waɗanda ake ƙara batun shari’ar.
Mai Shari’a Usman Na’abba ne ya ba da umarnin ɗage ƙarar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu bayan da lauyan mai gabatar da ƙara Y. A. Adamu ya sanar da kotun cewar dukkan yunƙurin da suka yi na sanar da waɗanda ake ƙara ya ci tura.
Sai dai lauyan Ganduje, Barista Musa Lawan ya ce tun da fari rashin sanar da su ƙarar da aka shigar ne ya sa suka ƙaurace wa zaman, amma yanzu suna jiran a sanar da su.
Gwamnatin Kano na tuhumar Ganduje matarsa da ɗansa da kuma wani abokinsa da aikata laifuka takwas, waɗanda suka danganci cin hanci da rashawa.
Latsa hoton ƙasa ku saurari ƙarin bayanin da lauyan Ganduje, Musa Lawan ya yi wa Khalifa Shehu Dokaji:
Comments