Posts

Hukumar EFCC na neman tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello ruwa a jallo

Image
Bayanan hoto, Tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello Ministan shari'ar Najeriya ya bayyana takaici kan yadda ya ce wasu 'yan siyasa ke kange kansu daga kamu bisa wasu laifuka da ake zargin sun aikata. Chief Lateef Olasunkanmi Fagbemi (SAN) ya bayyana hakan ne biyo bayan kulli-kurciyar da aka yi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da jami'an hukumar EFCC inda a 'karshe suka kasa damke shi sakamakon kange shi da ake zargin wani jami'in gwammnati ya yi. Al'amarin ya sanya Minstan shari'a ya gargadi jami'an gwamnati wadanda dokar 'kasa ke karewa su guji kawo cikas a kokarin da ya cancanci yabo da hukumar EFCC ke yi. Mai sharhi, Barrister Audu Bulama Bukarti ya bayyana cewar akwai bukatar wannan gargadi abu ne da ya zama wajibi. '' Ita hukumar EFCC, hukuma ce da dokar Najeriya ta kafa ta kuma ba ta ikon ta binciki wanda ake zargi da laifi kuma wanda ake zargi da laifin komai girmansa a 'kasar''. Barrista Bulama ya kuma kar...

NASIHOHI GUDA HAMSIN (50)

Image
1 ka kula da kanka 2 yazamana kana jin tsoron Allah 3 ka san cewa duk abinda ya sameka daga Allah ne 4 ka zamu mai cika alkawari 5 ka zauna da kowa lafiya 6 ka dinga tunawa da mutuwa 7 ka rage buri 8 ka cire kwadayi 9 banda yin hassada don kaga Allah ya daukaka wani 10 kasan cewa ita fa duniya ba matabbaciya bace 11 ka yawaita istigifari 12 ka yawaita salati ga manzon Rahama 13 banda yin gulma ko munafurci 14 banda cin amana 15 ka zauna da kowa lafiya 16 ka tsarkaka zuciyarka 17 banda nufar mutum da sharri 18 karkayi zalunci 19 karkayi girman kai 20 karkayi wulakanci 21 ka zama mai taimako 22 ka kula da addininka 23 ka zamu mutum mai Alkunya 24 ka zama mutum nagari mai kirki 25 kasan cewa komai mai wucewa ne 26 ka dinga hakuri kar ama shaidar cewa baka da hakuri 27 ka kuma yawaita addu'a 28 kayi biyyah ga iyayenka 29 ka zama mai tausayi 30 ka zama mai imani 31 kana aiki da hankalinka 32 ka guje wa sabon Allah 33 karka ci haram 34 karkayi shaye-shaye 35 ka nisanci zina 36 ka mai da ...

Kotun Kano ta É—age zaman tuhumar Ganduje

Image
Copyright: Socail Media Wata babbar kotu da ke Kano ta É—age sauraron tuhumar da gwamnatin jihar ke yi wa tsohon gwamna Abdullahi Ganduje kan cin hanci da rashawa. Bayanai sun nuna cewa kotun ta É—auki matakin ne saboda rashin sanar da waÉ—anda ake Ć™ara batun shari’ar. Mai Shari’a Usman Na’abba ne ya ba da umarnin É—age Ć™arar zuwa ranar 29 ga watan Afrilu bayan da lauyan mai gabatar da Ć™ara Y. A. Adamu ya sanar da kotun cewar dukkan yunĆ™urin da suka yi na sanar da waÉ—anda ake Ć™ara ya ci tura. Sai dai lauyan Ganduje, Barista Musa Lawan ya ce tun da fari rashin sanar da su Ć™arar da aka shigar ne ya sa suka Ć™aurace wa zaman, amma yanzu suna jiran a sanar da su. Gwamnatin Kano na tuhumar Ganduje  matarsa da É—ansa da kuma wani abokinsa da aikata laifuka takwas, waÉ—anda suka danganci cin hanci da rashawa. Latsa hoton Ć™asa ku saurari Ć™arin bayanin da lauyan Ganduje, Musa Lawan ya yi wa Khalifa Shehu Dokaji:

Yadda gwamnatin jihar Katsina ta rarraba wa jami'an tsaro motocin yaƙi

Image
  ASALIN HOTON, KATSINA STATE GOVERMENT Bayani kan maĆ™ala Marubuc Sanya sunan wanda ya Gwamnatin jihar Katsina ta rarraba motocin yaĆ™i ga jami'an tsaro domin shawo kan matsalar tsaro a Ć™ananan hukumomin da aka fi fuskantar hare-haren Ć´anbindiga. Gwamnan jihar Katsina Mallam Dikko Ummaru Radda ne ya Ć™addamar da rabon motocin a ranar Litinin. Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ta Katsina, Dakta Nasiru Mu'azu ya shaida wa BBC cewa sun yi la'akari ne da halin da ake ciki, kuma ita wannan mota mai sulke na taimaka wa wajen yaĆ™in da suke da Ć´an bindiga. Gwamnatin ta jihar Katsina ta rarraba motocin guda 10 ne ga jami'an tsaro na Ć´an sanda da sojoji da kuma Ć´an sa-kai da gwamnatin ta dauka a kwanakin baya domin taimakawa wajen yaĆ™i da Ć´an bindiga a jihar." ASALIN HOTON, KATSINA STATE GOVERMENT Mun yi maganin masu bai wa Ć´an bindiga bayanai-Gwamna Dikko Radda 11 Fabrairu 2024 Gane Mini Hanya tare da Gwamnan Katsina Dikko Radda 21 Oktoba 2023 'Ćłanbindiga ...

Fargaba ta ƙaru a ranar Asabar, yayin da jama'ar Iran suka shiga tsoro don gudun

Image
  Fargaba ta Ć™aru a ranar Asabar, yayin da jama'ar Iran suka shiga tsoro don gudun kada Isra'ila da mayar da Ć™awayen ta su martani. jama'a sun razana sosai ta yadda ake ta rige rigen siyan kayan abinci da man fetir da kuma sauran abubuwan buĆ™ata. An samu dogayen layin man fetir a gidajen mai da ke birnin Tehran da ma sauran manyan birane, yayin da jama'a suka cika manyan kantuna domin siyan kayan buĆ™ata, Duk da cewa Isra'ila ta yi IĆ™irarin cewa ta daĆ™ile kashi 99 cikin dari na makamai masu linzami da Iran ta harba mata, jami'an gwamnatoin Iran suna murna ne a kan abin da suka kira nasarar yin abin da ba a taÉ“a yi a can baya ba. Babban hafsan sojin Iran, Manjo Janar Mohammad Bagheri, ya bayyana cewa daga cikin wuraren da suka kai harin akwai harda wata barikin sojin sama, inda jirgin saman inda kuma daga can ne jirgin Isra'ila samfarin F35s ya tashi har ya yi sanadiyyar mutuwar dakarun Iran 7, a birnin Damascu. Ya bayyana yaqinin cewa Iran ta cimma nasarar a...

Yadda wani almajiri ya fille wa É—an shekara shida kai a Kano

Image
    Copyright: Other Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta fara gudanar da bincike kan al’amarin da ya biyo bayan zargin fille kan wani karamin yaro É—an shekara shida da wani almajiri ya yi a kauyen Kanwa da ke karamar hukumar Madobi. Rahotanni dai sun nuna cewa almajirin mai shekaru 22 ya kashe yaron ne a kusa da wata makarantar firamare kafin ya cire kansa. Kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Usaini Gumel ya shaida wa BBC cewa almajirin bayan ya yanke wa yaron kai ya jefa da kan a cikin wani masai. "A jiya ne aka wayi gari da wannan labari da ke cewa wasu masu ruwa da tsaki suka lura da cewa sun ga wani yaro a wannan Ć™auye da wuĆ™a wanda suka ga alamun jini a jikin wuĆ™ar kamar jinin É—an Adam ne, Hakan ne ya sa suka zarge abin da ya sa 'yan unguwa suka cafke shi, suka tasa shi gaba, sai suka ga gangar jikin mutum inda ya amsa shi ne ya kashe shi. Bayan da Ć´an sanda suka je, shi ne ya ja su ya kai su inda ya wurgar da kan, inda suka ga kan yaron." In ji kwamishinan 'ya...

Yau take sallah barka da sallah

Image
Ya ce ƙwarewarsu da rashin bai wa abokan kulɗa kunya wajen shirya abincin fita-kunya kamar tuwon sallah cikin gwaninta sun sa mutane na ƙara neman ƙwararrun masu dafa abinci. Ko ba komai, in ji shi, ba a ko'ina ake samun ɗanɗano da daɗi da iya tsara dafaffen abinci mai rai da lafiya a kwano, da ƙamshin burgewa ba. "A kawo muku har gida, ba tare da kun san wata wahalar da aka yi ba, kawai ci kuka sani" in ji mai gidan abincin. "Sai dai ku ci, ku ji daɗi, shi ma wanda aka ba, ya ci ya ji daɗi. Sai a yi ta tunanin ta yaya aka yi haka?" Mata da yawa kamar Ni'ima Ibrahim, ba lallai su yarda da wannan ra'ayi ba. Suna ganin duk da zamani, amma girki ya fi yarda da hannun mata. Hatta naƙaltar yadda ake shirya tuwon sallah, ba abu ne da ke buƙatar wuta-wuta da riƙon maza ba. Gwanintar mata ta fi tashi a girkin tuwon sallah Mata suna bai wa girkin tuwon sallah wata kulawa ta musamman, cewar Dr Hadiza Koko. "Mace du wadda take, in aka ce tuwon sallah za ta yi....

gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sake nada amb Yusuf imam ogan ɓoye

Image
  a matsayin Mai bashi shawara akan harkokin matasan da wasanni  tare da wasu mutum takwas Wanda zasu taimakawa Gwamnan a fanno daban daban . A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, a Wanan Rana yace Gwamnan ya amince da nada  1. Farfesa Ibrahim Magaji Barde, a matsayin mai bashi shawara na musamman kan harkokin tattara kudaden shiga (IGR).  2. Dr. Abdulhamid Danladi, mai bashi shawara na musamman kan harkokin kasashen waje II  3. Engr.  Bello Muhammad Kiru, mai bashi shawara na musamman kan albarkatun ruwa.  4. Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) ya sake nada shi a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni.  5. Dr. Nura Jafar Shanono an dauke shi daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Darakta, a ma.aikatar Ruwa da Gine-gine (WRECA).  6.Haka kuma Baba Abubakar Umar ya samu sauyi daga mai bawa gwamna Kano shawara na musamman ga harkokin makarantu mas...

Shin me ya sa ƙasashen yammaci ke shakkar manhajar Tiktok?

Image
kasar China ta soki wani kuduri da 'yan majalisar Amurka ke yi wa karatu wanda kuma zai iya kai wa ga haramta amfani da kafar Tiktok a Amurkar, wani abu da Chinar ta bayyana da rashin adalci. Wannan ne dai mataki na baya-bayan a shekarun da kasashen biyu suka kwashe suna zaman tankiya dangane da fargaba kan manhajar wadda wani kamfanin kasar China ya mallaka. Kasashen yammaci da dama dai sun haramtawa jami'ai da 'yan siyasa da jami'an tsaro sauko da manhajar ta Tiktok a na'u'rorin gwamnatocinsu. Shin wadanne dalilai ne ke sa ake shakkar wannan manhaja ta Tiktok? Sannan ta yaya kamfanin ke magance su?. Ga wasu dalilai guda uku. 1. TikTok na karɓar bayanai masu yawa daga abokan hulda TikTok ya ce tsarin karbar bayanai na manhajar na gudana ne bisa yadda ake yi a duniya fasahar sadarwa. Masu suka na yawaita sukar Tiktok da tara bayanai masu yawa. Wani rahoton tsaro na intanet da wasu masu bincike na kamfanin Internet 2.0 na kasar Australia suka wallafa a watan Yuli...