Sojojin Najeriya sun kashe 'yan bindiga a Neja da Borno
ASALIN HOTO Rundunar sojin Najeriya ta ce ta dakarunta sun samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama a jihohin Borno da Neja. Cikin wata sanarwar da mai magana da yawun rundunar sojin saman Æ™asar, Edward Gabkwet ya ce cikin jerin wasu hare-hare ta sama da dakarun rundonin Hadin Kai da Whirl Punch suka Æ™addamar a jihohin biyu ya samu narasar lalata wasu shirye-shiryen 'yan bindigar. Edward Gabkwet ya ce a ranar 3 ga watan Mayu dakarun Æ™asar sun kai hari a garin Chinene da ke yankin tsaunin Mandara da ke kusa da jihar Borno. Ya ce dakarun sojin Æ™asar sun ga 'yan bindigar na wani taro da ake kyautata zaton tattaunawa suke yi a lokacin da jirgin sojin ya kai musu hari tare da kashe su. “Haka kuma a garin sojojinmu sun hangi wasu motocin yaÆ™i bakwai da ake zaton na 'yan bindigar ne a Æ™arÆ™ashin wata bishiya, nan take su ma aka kai musu hari tare da lalata su'', in ji sanarwar. Sanarwar ta Æ™ara da cewa “bayanan da muka samu bayan hare-haren sun nuna cewa an samu nasara...

Comments