Posts

Falasɗinawa sun shiga fargaba gabanin hare-haren Isra'ila ta ƙasa a birnin Rafah

Image
ASALIN HOTON, EPA-EFE/REX/SHUTTERSTOCK Sa'o'i 3 da suka wuce Wani likita Bafalasɗine a birnin Rafah ya ce mutane sun kaɗu sosai saboda fargabar sabbin hare-haren Isra'ila, ta ƙasa, waɗanda ta ƙaddamar a Rafah, ɗaya daga cikin manyan birnin kudancin Gaza. a jerin saƙonnin da ya aikewa BBC , Dr Ahmed Abuibaid ya ce hare-haren saman su ƙazance, kuma sun shafi kusan dukkan sassan birnin. Ya ce "Tambayar da ta fi yawo a zukatan mutane a halin yanzu ita ce ina zamu?" A makon jiya ne Firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya sanar da kutsawar dakarunsa Rafah ta ƙasa, yana mai cewa za su faɗaɗa hare-hare. Fiye da rabin jama'ar Gaza da yawansu ya miliyan biyu ne yanzu haka suke zaman hijira a birnin Rafah mai maƙwabta da kan iyakar ƙasar Masar, duk da cewa mutane dubu 250 ne kacal ke rayuwa a birnin kafin ɓarkewar yaƙi tsakanin Isra'ila da ƙungiyar Hamas, a cikin watan Oktoban bara. Mafi yawan mutanen su na zaune ne cikin mawuyacin hali na rashin muhalli da...

Tinubu ya ƙaddamar da sabbin jiregen yaƙi don magance matsalar tsaro

Image
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya jaddada aniyarsa ta kawo ƙarshen mastalar tsaro a ƙasar ta hanyar ƙaddamar da wasu sabbin jirage masu saukar ungulu kirar T-129 ATAK guda biyu da kirar King Air 360ER Beechcraft a barikin sojin saman Najeriya da ke birnin Makurdi a jihar Benue.. Da yake magana ta bakin mataimakin shugaban kasa Sanata Kashim Shettima, shugaba Tinubu ya bayyana kwarin gwiwar sayen waɗannan sabbin jiragen masu saukar ungulu domin inganta yaƙin da rundunar sojojin saman Najeriya ke yi a ƙasar da yankin yammacin Afirka. Badaru Abubakar, ministan tsaro ya yaba wa ƙoƙarin shugaba Tinubu na mayar da zaman lafiya a fadin ƙasar, ya kuma gode masa bisa jajircewarsa da goyon bayan da yake bai wa rundunar sojin ƙasar duk da kalubalen da take fuskanta.

Mun yi maganin masu bai wa ƴan bindiga bayanai-Gwamna Dikko Radda

Image
ASALIN HOTON, DIKKO RADDA/FACEBOOK Sa'o'i 5 da suka wuce Gwamnan jihar Katsina ya yi kira ga jama’ar jihar su tallafawa jami’an tsaro wajen yaƙi da ƴan bindiga da suka addabi sassan jihar. Gwamnan Umaru Dikko Radda ya ce akwai buƙatar mutane, musamman matasa su haɗa kansu domin tallafawa jami’an tsaro wajen aikin kawar da matsalar tsaron. A hirar sa da BBC, gwamnan ya kuma musanta rahotannin da ke cewa gwamnatinsa ta gaza kare rayuka da dukiyoyin al’umma yayin da ƴan bindiga ke cigaba da kai hare hare a wasu yankunan jihar. Gwamnan ya ce tun bayan da ya karɓi mulki, gwamnatinsa ta samu nasara sosai a yakin da take yi da ƴan bindiga, ciki har da kafuwar rundunar tsaro ta musaman wadda a cewarsa ta taimaka wajan dakile hare haren yan bindigar. Ya ce: "Mutumin Jibia da mutumin Batsari da na Kankara da na Danmusa da na Sabuwa da na Faskari da na Dandume sun san cewa an samu sauƙi a matsalar tsaron da muke fuskanta a jihar Katsina’’ Ya yi bayanin cewa sabbin dabarun...

Enzo na son Barcelona, Chelsea da Utd da PSG na ribibin Frenkie de Jong

Image
Sa'o'i 2 da suka wuce Ɗanwasan tsakiya na Argentina Enzo Fernandez, mai shekara 23, na son raba gari da  Chelsea  ya koma  Barcelona  duk da kwangilarsa sai 2032 za ta kawo ƙarshe a Stamford Bridge. (Sport - in Spanish) Bayern Munich  ta saka ɗanwasan  Fulham  da Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28, cikin jerin ƴanwasan tsakiya da take hari a bazara. (Bild) Liverpool  na sa ido kan ɗanwasan  Fulham  da Ingila mai shekara 26 Tosin Adarabioyo. (90min) Liverpool  kuma na son ɗauko ɗanwasan baya na  Fulham  da Amurka Antonee Robinson, mai shekara 26, domin maye gurbin Andy Robertson, mai shekara 29. (Fichajes - in Spanish) Ɗanwasan baya na  Bournemouth  Lloyd Kelly, mai shekara 25, na dab da zuwa  Liverpool  ko  Tottenham,  a yayin da  AC Milan  da  Juventus  da sauran ƙungiyoyin Jamus ke ribibin ɗanwasan na Ingila. (Football Insider) Barcelona  ta tuntuɓi E...

Abubuwan da JNI ta faɗa kan tsadar rayuwa a Najeriya.

Image
Sa'a 1 da ta wuce Kungiyar Jama’atu Nasrul Islam ta nuna damuwa kan matsalar hauhawan farashin kayayyakin abinci da ake fuskanta a Najeriya. Kungiyar ta bukaci mahukuntam kasar da su  gaggauta daukar matakan tallafawa al’umma don rage musu wahalhalu da suke fama da su. A cikin wata sanarwa da ta fitar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin mai alfarma sarkin musulmi Sultan Muhammadu Sa'ad Abubakar na uku ta ce abin damuwa ne kan yadda wasu al'umma suka fara zanga-zanga sakamakon mawuyacin halin da suke ciki. Ta ce yadda mutane suka fara harzuƙa na nuna cewa tura ta kai bango, kuma ishara ce ga mahukunta su ɗauki matakin gaggawa domin gudun kada al'ammura su gagari kundi Ta bukaci gwamnati da ta gaggauta daukar matakan tallafawa al’umma don rage musu raɗaɗi.

Majalisar wakilan Najeriya za ta ƙarfafa dokar ɓata-sunaKakakin majalisar wakilan Najeriya,

Image
Tajudeen Abbas ya ce majalisar za ta ƙarfafa dokar ɓata-suna da cin cin mutuncin mutane da kuma cin zarafin mutane ta intanet. Honarabul Tajedeen ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai kan abubuwan da ke damun ƙasar da aka gudanar a wani ɗakin taro a harabar majalisar. Kakakin majalisar ya ce manufar dokar ba zai ci karo da 'yancin faɗar albarkacin baki, amma za ta kare mutane da hukumomi daga cin zarafinsu a intanet. Ya ƙara da cewa dole ne 'yan Najeriya su damu bisa yadda ake yawan cin zarafin jami'an gwamnati a shafukan intanet. Honarabul Abbas ya bayyana yadda kakakin majalisar da ya gabace shi, Femi Gbajabiamila, ya kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka fuskanci cin zarafi da intanet, da ɓata suna

NNPCL ya musanta shirin ƙara kuɗin man fetur

Image
Getty Images Copyright: Getty Images Kamfanin mai na Najeriya NNPCL ya musanta duk wani yunƙuri na ƙarin farashin man fetur a faɗin ƙasar. A baya-bayan nan masu ababen hawa na fuskantar dogayen layuka a wasu gidajen mai a wasu yankunan ƙasar, musamman a kudancin ƙasar, sakamakon fargabar da ake yi cewa hukumomi za su ƙara farashin man. To sai dai a cikin wata sanarwa da kamfanin mai na ƙasar, NNPCL ya fitar mai ɗauke da sa hanun jami'in hulɗa da jama'a na kamfanin, Olufemi Soneye ya fitar, ya buƙaci 'yan ƙasar su kwantar da hankalinsu. ''Ba za a ƙara kuɗin man fetur ba'', kamar yadda sanarwar kamfanin ta tabbatar. “NNPC Ltd na buƙatar 'yan Najeriya su yi watsi da duk wata jita-jita da ta dangancin ƙarin kuɗin mai, kuma kamfanin na son tabbatar wa 'yan ƙasa cewa babu wani yunƙuri da hukumomi ke yi game da ƙarin kuɗin man'', in ji sanarwar. Tun bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin ƙasar ta yi cikin watan Mayun shekarar da ta gabata, faras...
Image
  Gazawa ce APC ta fito tana zargin ƴan'adawa" ASALIN HOTON, FACEBOOK/ATIKU ABUBAKAR/PETER OBI Sa'o'i 3 da suka wuce Jam'iyyun adawar Najeriya sun mayar wa APC mai mulki martani, kan zarginsu da hannu wajen tunzura jama'a domin yi wa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bore. Lamarin ya biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a jihohin Kano, da Neja da Legas, kan tsadar rayuwa. Sai dai a cewar jam'iyyun adawar jama'iyyar APC ce a kan mulki, don haka alhakin tabarbarewar lamurra a kasar ya rataya ne a wuyanta. Manyan jam'iyyun adawar Najeriya PDP da LP, sun ce cunar rigar jam'iyyar APC ce ke neman kayar da ita, kuma tun farko kankanba ce ta kai ta ga neman sahalewar 'yan Najeriya domin jagorantarsu, ba tare da wani tartibin tsarin yaye musu matsalolin da suke ciki ba. TALLA Shi ya sa a yanzu bayan shafe kusan shekara guda a kan Mulki da shugaba Tinubu ya yi, take zarginsu da yi wa gwamnati shune, kamar yadda jam'iyyun biyu suka bayyana. Mat...

Abinci bakwai da ƴan Najeriya suka sauya saboda tsadar rayuwa

Image
Sa'o'i 3 da suka wuce Sakamakon tashin gwauron zabbin kayan masarufi da 'yan Najeriya ke fama da shi wanda matsin tattalin arzikin da kasar ke fuskanta ya haifar, yanzu haka mutane da dama ba sa iya samun abinci sau uku a kullum. Bayanai sun nuna cewa su kansu wadanda suke samun ukun a kowace rana, sun sauya daga abin da suka saba ci a baya zuwa mai sauki wanda za a saya da kudi kadan sannan kuma zai cika ciki. Daga bayanai da kuma binciken da BBC ta yi a kasuwanni, ga wasu jerin abinci ko kuma kayan hadin abinci guda bakwai da yanzu jama'a suka sauya domin samun sa'ida: Shinkafa:  Yanzu haka magidanta da dama sun koma amfani da wata nau'in shinkafa da ake wa lakabi da "A Fafata". Ita wannan shinkafar dai ta yi kama da wadda a zamanin baya lokacin wadata ake kira "dameji" wato wadda kamfani ya fitar saboda ta lalace. Bayanai sun nuna ana sayar da kwanon irin wannan shinkafa ta "A fafata" naira dubu biyu da dari biyar. ASALIN HOTON, ...

Tsohon Gwamnan Jihar Yobe Bukar Abba ya rasu

Image
ate Gv Copyright: Yobe State Gov Gwamnatin Jihar Yobe ta sanar da mutuwar tsohon Gwamnan jihar Sanata Bukar Abba Ibrahim. Cikin wata sanarwa da Gwamna Mai Mala Buni ya fitar ta hannun daraktan yaɗa labaransa Mamman Mohammed, ta ce ya mutu ne a Saudiyya bayan wata doguwar lafiya da ya yi fama da ita, sannan kuma za a binne shi a can. Gwamna Mai Mala ya yi umarnin a gudanar da zaman makoki kamar yadda aka saba a al'adance kuma gwamnati ce za ta gudanar da hakan ga marigayin. Mai Mala ne zai ci gaba da karɓar ta'aziyyar marigayin a masallacin gidan gwamnatin jihar da ke Damaturu. Gwamna Bini ya bayyana mutuwar a matsayin gagarumin rashi ga gwamnati da kuma mutanen jihar. "Wannan ba ƙaramin rashi ba ne muka yi, amma haka Allah ya so, shi nemahaliccinmu, muna fatan ya yi masa gafara," in ji sanarwar. Marigayi Bukar Abba wanda ya wakilci Yobe ta Gabas a matsayin Sanata, ya mutu yana da sheka75.