Gazawa ce APC ta fito tana zargin ƴan'adawa"

.

ASALIN HOTON,FACEBOOK/ATIKU ABUBAKAR/PETER OBI

Jam'iyyun adawar Najeriya sun mayar wa APC mai mulki martani, kan zarginsu da hannu wajen tunzura jama'a domin yi wa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu bore.

Lamarin ya biyo bayan zanga-zangar da aka gudanar a jihohin Kano, da Neja da Legas, kan tsadar rayuwa.

Sai dai a cewar jam'iyyun adawar jama'iyyar APC ce a kan mulki, don haka alhakin tabarbarewar lamurra a kasar ya rataya ne a wuyanta.

Manyan jam'iyyun adawar Najeriya PDP da LP, sun ce cunar rigar jam'iyyar APC ce ke neman kayar da ita, kuma tun farko kankanba ce ta kai ta ga neman sahalewar 'yan Najeriya domin jagorantarsu, ba tare da wani tartibin tsarin yaye musu matsalolin da suke ciki ba.

Shi ya sa a yanzu bayan shafe kusan shekara guda a kan Mulki da shugaba Tinubu ya yi, take zarginsu da yi wa gwamnati shune, kamar yadda jam'iyyun biyu suka bayyana.

Mataimakin kakakin babbar jam'iyyar adawa ra Najeriya PDP na kasa Malam Ibahim Abdullahi, ya ce " APC ta sauka ta ba su mulkin ta koma tana zuga da tunzura al'umma idan tana ganin hakan shi ne daidai."

"Talaka na ciki halin ha'ula'i na mummunan rashin tsaro, da ƙangi na talauci da ƙunci na rashin inda zai saka gaba, amma a ce bai da ikon ya fito ya faɗi halin da yake ciki, sai gwamnati ta zargi jam'iyyun adawa, wannan rainin wayau ne a buge ka kuma a ahanaka kuka," in ji Malam Ibrahim.

A cewarsa. " kowa a Najeriya ya san halin da ake ciki, a gwamnatance APC ta gaza gaza, ba su iya ba."

Irin wannan martani ne ita ma jam'iyyar adawa ta Labour ta mayar, tana mai nuni da cewa kamata ya yi APC ta zargi kanta, ba wai zargin ƴan'adwa ba

Kakakin jam'iyar LP na ƙasa Dr Tanko Yunusa ya ce " Su ne da kan su suka tunzura mutane saboda sun yi wa al'umma ƙwace, sun saka su cikin yunwa, sannan an hana su magana, kun hana su zuwa makarantu, kun ce kada su je gona saboda riƙon sakainar kashi da suka yi wa mutane."

Dr Tanko ya ce da gwamnati ta yi abin da ya dace da ba a samu matsalar da ake fuskanta ba.

"Yanzu dala ta kai 1,500 , yanzu mu ne muka yi haka? mu ne a gwamnati ? kuma su ma ƴan Najeriya wayayyi ne, ko ana nufin ba su san ƴancin kansu ba? sun nuna sun gaza, saboda da mulkin Buhari da na Tinubu kamar Ɗanjuma ne da ɗanjummai," in ji Dr Tanko.

Comments

Popular posts from this blog

An ga watan Azumin Ramadan a Saudiyya

Tinubu zai jagoranci taron yaƙi da ta'addanci na Afirka a Abuja

Yadda wani almajiri ya fille wa ɗan shekara shida kai a Kano